Adadin mutanen da cutar Kwalara ta kashe a Abuja, babban birnin kasar sun kai 60 kamar yadda mahukunta suka tabbatar.
Tun a ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata ne cutar ta soma bulla inda ta yi ajalin akalla mutum 7 daga cikin 91 da ake zargin sun kamu da ita.
- Bethel Baptist: Dalibai 2 sun tsere daga hannun ’yan bindiga
- Dalilin da Sakkawata ke al’adar gasa dabbobi a lokacin sallah
Karamar Ministar Abuja, Dokta Ramatu Tijjani Aliyu, ta tabbatar da adadin mamata da kuma yadda cutar ke yaduwa a yankun Pyakasa da Gwagwa da ke birnin na Abuja.
Cikin sanarwa da mai magana da yawun Ministar, Mista Austin Elemue ya fitar, ta ce an samu karin wadanda suka kamu da cutar daga 604 zuwa 689 cikin sa’o’i 72 da suka gabata.
A cewar Ministar, yankunan da aka samu mamatan sun hada da Karamar Hukumar Cikin Birni da Kewaye wato AMAC inda mutum 22 suka mutu, sai kuma Bwari inda aka samu mamata 22.
An kuma samau mutum 9 da suka riga mu gidan gaskiya a Gwagwalada, sai mutum 4 a Kuje da kuma mutum 3 a Kwali.
Da take bayyana rashin jin dadinta kan lamarin, Ministar ta ce ba za ta sabu ba su ci gaba zura idanu kan wannan cuta mutane suna mutuwa alhali ana iya kiyaye faruwar hakan.