✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwalara ta kashe mutum 4, ta kama 48 a Gombe

Cutar dai ta barke ne a wasu unguwanni na Karamar Hukumar Gombe.

Akalla mutum 48 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Kwalara, hudu kuma sun mutu bayan bullar cutar a Karamar Hukumar Gombe da ke Jihar Gombe.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Habu Dahiru ne ya ayyana bullar cutar ga manema labarai ranar Talata, inda ya ce an sami rahoton barkewarta a wasu unguwanni na Karamar Hukumar.

A cewarsa, unguwannin sun hada da Bolari ta Gabas da ta Yamma da Jekadafari da Pantami da Kumbiya-kumbiya da Herwagana da Shamaki da Nasarawo da Kuma unguwar Dawaki.

Dokta Dahiru, ya ce tuni suka sanar da Gwamnan Jihar halin da ake ciki, inda ya ba su umurnin daukar matakin kariya don gujewa yaduwarta a sauran sassan Jihar.

Kwamishinan ya ce tun a tsakanin watannin Yuni da farkon Agustan 2021 suka sami rahoton barkewar cutar a wasu Kananan Hukumomi guda hudu da suka hada da Balanga da Yamaltu-Deba da Dukku da Kuma Gombe.

Sai dai ya ce bayan yin gwaje-gwaje a lokacin, an gano ba asalin tarar cutar ta Kwalara ba ce.

Daga nan sai Kwamishinan ya ja hankalin mutane kan su tabbatar suna tafasa dukkan ruwan da za su sha don kauce wa kamuwa da cutar.

A bangaren muhalli wanda shi ma yake da alaka da cutar, Kwamishinan ya ce Ma’aikatarsa ta hada gwiwa da takwararta ta Muhalli wajen hana zubar da shara barkatai wanda shi ma zai taimaka matuka.

Dokta Dahiru ya kuma yi kira ga jama’a da su fara bayar da ruwan gishiri da suga ga duk wanda suka ga alamun ya kamu da cutar, inda ya ce hakan na taimaka wa matuka a matsayin taimakon farko kafin a kai shi zuwa asibiti.