Cutar kwalara ta yi sanadiyar mutuwar mutum 2,791 a jihohi 28 da Yankin Birnin Tarayya tun farkon wannan shekara, in ji Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC).
Hukumar ta NCDC, a wani rahoton da ta fitar ranar Talata, ta ce mutum 81,413 aka samu labarin sun kamu da cutar a wannan lokacin.
Jihohin da abin ya shafa su ne: Adamawa, da Bauchi, da Bayelsa, da Binwuwai, da Borno, da Kuros Riba, da Delta, da Ekiti, da Enugu, da Gombe, da Jigawa, da Kaduna, da Kano, da Katsina, da Kebbi, da Kogi, da Kwara, da Nasarawa, da Neja, da Ogun, da Osun, da Filato, da Sakkwato, da Taraba, da Yobe, da Ribas, da Zamfara, sai kuma Yankin Babban Birnin Tarayya.
“Zuwa 19 ga Satumba, 2021, jimillar mutane 81,413 ne aka bayar da rahoton sun kamu yayin aka bayar da labarin mutuwar mutum 2,791 daga jihohi 28 da Yankin Babban Birnin Tarayya.
“Daga cikin wadanda aka bayar da labarin sun kamu tun farkon shekarar, yara maza da mata ’yan shekara 5 zuwa 14 ta fi shafa,” inji rahoton.
Hukumar ta kuma ce kashi 50 cikin 100 na wadanda aka ba da rahoton sun kamu maza ne, kashi 50 mata.