✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwalara ta kashe 20 wasu 322 sun harbu a Bauchi

Cutar amai da gudawa ta bulla a kananan hukumomi tara a Jihar Bauchi

An tabbatar da rasuwar mutum 20, wasu 322 kuma sun harbu bayan barkewar annobar amai da gudawa a kananan hukumomi tara a Jihar Bauchi.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Aliyu Mohammed Maigoro, ya sanar a safiyar Talata cewa an samu bullar cutar kuma an tattara samfur 21 wadanda 19 daga ciki suka nuna akwai kwayar cutar ta amai da gudawa mai suna V-Cholera.

Ya ce mutumin da aka fara samu yana dauke da cutar wani matashi ne mai shekara 37 wanda ya je Babban Asibitin Burra a ranar 24 ga watan Afrilu, 2021.