A watan Yawon-wulli
An shata kasurwar tubali
A hada-hadar tozali
Tushen cinikin asali
Ba daukar matsabbai ai fatali
Komai a yi shi da hankali
Hanyar gayauna a bi lawali
Makiyaya babu jangali
An yi wa haja kulli
Don kauce wa jidali
Rubutun baki da wasali
Almajirai a kan dakali
Zuge da karo na walwali
Zayyanar allo mai kama da sifili
Wata kamar zanen muhalli
Ababakar, Umar, Usman da Ali
Sahabbai jagororin koyin Maghili
Mai imani da tawakkali
Zakkah, sadaka babu aikin zumbuli
Rafkanuwa ke sa ba’adi ko kabli
A hau dandamali
Wasu sun karke a dandali
Suna ta gantali
Adon gari na gadar fi’ili
’Yan lalle sun taka a fili
A koyi sana’a
Don neman sa’a
Talalar talauci a ce a’a
Baudadun miyagu masu ba’a
Alwalarsu tai lam’a
Masu tafka masha’a
Aikin assha babu kana’a
Mutanen kwarai ke kira’a
Ba sa keta shari’a
Sai a kada musu kuri’a
Katin zakulo Hauro
Ramin takardun kudi a tutturo
Lambobi aka kirkiro
Sai dami ya zuraro
Shan kan kwacen kwararo
Harobiyawa a kula
Da ’yan wala-wala
Masu kawo tarnakin walwala
Su samfe da salala
Da zarar sun ga galala
Ai ta cakumar cin kwala
Har wasu su hassala
Sui wa juna gula
’Yan wanki sun shafa bula
An maishe da wani gaula
Yankan fatara da kansakali
Cikin natsuwa da hankali
A ci dadi da cokali
Bisashe na bin burtali
Babu kaya ko cabalbali
Ina direban alli
Aikinka ya zam na kamili
Kar kai rowar zumbuli
Kususan in kana da hali
Kai rabo balli-balli
Mu zamto masu tattali
Ai lissafin fidda jadawali
A fasko yawan na kasa da koli
Magance bala’in balbali
A iya shagali ban da izgili
Ranar tukunyar dambu
Ga watan madambacin dambu
karamin laujen silin dambu
An baje mana babban kitabu
Don koyon yaki da babu
Tarbiyyar addini
Ta hori mai sukuni
Ya jadadda imani
Ya bai wa masu ba ni- ba ni
Da maharumin da yai wa kansa hani
Tallata haja dalla-dalla
Ai ta kwakwar shela
An kirawo mai ’yar tsala
Ta sauke mana kwalla
Mu saya a ba mu salala
Fitowar makwalashe filla-filla
Saye da sayarwa ba wahala
A kasuwa ana shagala
Bisashe an musu talala
Ana ta kirga kudi malala
Zamantakewa in an zauna
Hada-hadar kurtun magana
A na’ura a kan gana
Tai ta batu da zayyana
Shige da ficen Hauro ta nuna
Ciniki in an kulla
Babu kulla-kulla
Ko sa wani kwalla
kidayar kai-kawon kwandala
Kusu ya sha bulala
An shammaci ’yan damfara
Masu murguda wuya da makara
Damin dukiya sui ta zara
Zaluncinsu ya zarta na kura
Kullum suna ta tada kura
Sun cutar da masu furfura
Sun ki barin al’umma ta sarara
Suna ta jido a buhun algarara
Miyagu masu tijara
Rashin imani ba sa kaffara
Sui kwado da dara
Sun kyakyata sun dara
Al’umma a mummunar marra
An ja wasu sun tafka asara
Kun ji ta’adar masu fitsara
A wannan marhala
A kiyayi ’yan wankin gassala
Masu sa wa jiki kasala
Tare da tsallen tsula
Har ai ta lalala
A inganta alala
Tallarta ta zam ba illa
Masu saye su lula
Motsa mukamukin mamula
Har da karkata hula
Jinko kudin su
Ka tara a asusu
Maganin samarin kusu
Masu maishe da mutum sususu
A dumuiniya sun yi busu-busu
Sabon salon zamani
Yai hani
Ga masu satar sani
Da ke damfara a kasuwanni
A ingiza su sui ta wuni-wuni
Karkara da birni
Sun daina gani
Balle a gan su bini-bini
Kashedin iyaye da kakanni
’Ya’ya a nemi sani
kwakwar talla
Kwakin tela
kulla-kullar jela
katon tulu a tuttula
kulalan kulu a tattala
Harkace marar matsala
A dai jira talge ya sulala
Kitif-kitif miya a tsumbula
Balle ai tsumulmula
Ai wa tabahuwa dukan ta-mola