✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

‘Kuyangu 83 Shekau ya mutu ya bari a duniya’

Ya ce da yawa daga cikin mabiyan sun yi nadamar bin Shekau din

Wasu Kwamandojin kungiyar Boko Haram sun ce tsohon jagoran kungiyar, Abubakar Shekau, ya mutu ya bar kuyangu 83 kafin ya bar duniya.

Aminiya ta rawaito cewa Shekau ya rasu ne a watan Mayun 2021, yayin wata arangama da wata kungiyar ’yan ta’addan a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

To sai dai da yake jawabi a Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno, mai ba Gwamnan jihar shawara kan al’amuran tsaro, Birgediya-Janar Abdullahi Ishaq, ya ce wasu daga cikin makusantan Shekau din ne suka ba shi labari a kan kuyangun bayan sun mika wuya.

Ya ce, “Mun fara neman hanyar maganin ‘yan ta’adda ta ruwan sanyi kimanin wata 16 da suka wuce, jim kadan da mutuwar Abubakar Shekau, kuma gwamnati ba ta son ISWAP ta ci gaba da amfani da mayakansu. Mun san hakan na da matukar hatsari.

“Amma daya daga cikin mayakan da muka karba a Bama, ya shaida mana cewa Shekau ya mutu ya bar kuyangu 83. Ku ji fa, wai kuyangu 83!

“Sun ce yanzu haka yana wuta saboda ya aikata zunubi yayin arangamarsu da daya bangaren. A kullum yakan fada musu su fita su yi yaki, idan aka kashe su, ’yan matan Aljanna na jiransu,” inji shi.

Ya kuma ce mayakan da dama sun yi nadamar bin Shekau din, inda suka ce ya batar da su.

Birgediya-Janar Abdullahi ya kuma ce da yawa daga cikin mabiya Shekau din ko Alwala ba su iya yi ba, ballantana Sallah, sai da suka dawo da su Maiduguri sannan suka koya musu.