Mutum 836 sun warke daga cutar coronavirus a ranar guda a kasar Kuwait, lamarin da ya kai adadin wadanda suka warke zuwa 48,381 a kasar.
Sai dai karin mutum 553 sun kamu da cutar a ranar ta Juma’a, wanda ya kara yawan wadanda suka kamu a kasar zuwa 58,221.
Ma’aikatar Lafiyar Kuwait ta ce wadanda cutar ta kashe sun karu zuwa 404 sakamakon mutuwar mutum biyu a ranar, yayin da mutum 143 daga masu cutar ke cikin mawuyacin hali.
Kakakin ma’aikatar Dakta Abdullah Al-Sanad ya ce 219 daga cikin sabbin masu cutar ’yan kasar ne, sai kuma ’yan kasashen waje guda 234.
A jawabinsa kan cutar a kasar, Dakta Abdullah ya ce yawancin sabbin masu cutar sun harbu daga masu cutar a baya. Ana kuma gudanar da bincike domin gano dalilin kamuwar wasu mutanen.