Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Najeriya, ta cafke wasu mutum 10 da ake zargi da aikata laifin kutse a yanar gizo a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Kakakin Hukumar reshen jihar Ribas, Wilson Uwujaren ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai cikin birnin Fatakwal a ranar Laraba.
- NAFDAC ta karrama Shugaban Hukumar KAROTA a Kano
- An yi zanga-zanga kan yunkurin mayar da mafi karancin albashi hannun Gwamnoni a Kano
- Kotu ta tsare wanda ya yi wa yarinya mai shekara 10 fyade
Ya ce mutanen da aka cafke ana zarginsu da damfarar jama’a ta hanyar satar bayanai a yanar gizo domin wawusar kudi da kadarori.
“An cafke wadanda ake zargin ne a wani gida mai lamba 23 da ke lungun Sam Mba a unguwar God City da ke kusa ta titin NTA Akparale a birnin na Fatakawal.”
“An kama su ne bayan tattara bayanan sirrin da aka samu game da zarginsu da hannu a aikata zamba ta yanar gizo,” in ji shi.
Mista Uwujaren ya lissafo kayayyaki da aka samu a hannun ababen zargin da suka hada da motoci na alfarma guda uku, wayoyin salula 11, komfutar tafi da gidanka 4, katukan ATM da sauransu.
Kakakin hukumar ya ce za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar sun kammala binciken da ake gudanarwa a kansu.