Assalamu alaikum ma’abota bin wannan fili mai tarin albarka na iyayen giji da ke kokarin ganin an fadakar gami da ilimantarwa don samun ingantacciyar al’umma.
RABE-RABEN SAKI:
Da yawa mutane na yin kuskure game da saki, wani lokaci ma aure na karewa ba da sanin ma’aurata ba don sun jahilci abin.
Kamar yadda na sha yin bayani a baya cewa aure ibada ne, haka saki yana daga cikin ginshikin aure wanda yake da matukar sarkakiya.
Wadansu malaman na ganin cewa saki haramun ne amma mafi ingancin magana saki in har ya cika sharuddan da aka gindaya kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya zayyano su a cikin surar da ta yi magana a kan saki (Addalak) ba za a ce haramun ba, inda haramci zai shigo shi ne yayin da aka keta dokar Allah a ciki.
Zan kawo rabe-raben saki kamar yadda malamai suka yi bayani kamar haka:
1.Akwai saki na Sunnah: Shi ne a saki mace bayan ta gama haila ta tsarkaka kuma ya kasance ba a sadu da ita ba.
2. Saki na bidi’a: Shi ne a saki mace tana cikin jinin al’ada ko na haihuwa, ko bayan ta yi tsarki an sadu, haka nan saki uku a kalma daya ko a rarrabe amma a take.
3. Saki na kome: Shi ne sakin da bai kai uku ba. A nan hakkin miji ne idan ya so sai ya mayar da matarsa bayan ya auku, koda ba ta yarda ba, matukar ba ta gama idda ba wajibi ne ta koma. Kuma Sunnah ce ya sa shaidu a kan haka.
4. Saki bayyananne: Koda ba a yi niyya ba muddin aka furta ya tabbata , kamar ya ce ‘na sake ki’ ko ‘ke sakakka ce.’
5.Saki na kinaya: Kamar ya ce “fita daga gidana,’ ko ‘tafi gidanku’ amma fa da sharadin ya yi niyyar saki a ransa , amma in ba da niyyar saki ba ne, to irin wannan furuci ba ya zama saki.
Amma da zai ce ke wofintacciya ce ko kuwa kin halatta ga wadansu mazan to ta saku kuma babu kome a cikinsa har sai ta auri waninsa.
6. Sakin zabi: Shi ne miji ya ba mace zabi na zama da shi ko rabuwa, to idan har ta zabi rabuwar saki ya tabbata.
7. Saki na rubutawa a takarda ko wakilta wani ya rubuta ya ba ta, shi ma saki ya tabbata.
8. Saki na haramta wa kai: Idan mutum ya ce wa matarsa ke haramun ce a wurina ko kin haramta gare ni inda niyyar saki ne to ya tabbata, idan kuma niyyar ta zihari ce to ya yi kaffarar zihari sannan ta sake halatta a gare shi.
9. Sakin da babu kome: Ya kasu kashi biyar:
Saki uku da khul’i (mace ta fanshi kanta da wasu adadin kudi)da li’ani da sakin da alkali ya raba don rashin alherinsa da gabanin tarewa.
Zan dakata a nan a darasi na gaba in Allah Ya hukunta zan zayyano sharuddan da ake bi kafin mutum ya furta saki wanda masu bibiye da ni a cikin manyan dalilan da ke kawo mutuwar aure na yi bayani a kan rashin bin ka’idar Musulunci yayin saki kamar yadda ya zo a cikin Suratul Dalak.
Allah Ya amfanar da mu a kan abin da na furta kuma in yi dace a kan daidai,wanda na kuskure ina neman Allah Ya fahimtar da ni kuma Ya gafarta mana.
Sanusi Hashim Abban Sultana
08065507271