Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya ce sukar da ake yi masa ba zai tilasta masa janye goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu ba.
Rarara ya bayyana cewa ba zai juya wa shugaban kasar baya ba ne a yayin wata hira da aka yi da shi a kafar DLC Hausa.
A kwanakin baya Facebook ya rufe shafin mawakin bayan masu goyon bayan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya sun kai karar shafin nasa.
Sai dai a yayin tattaunawar, Rarara ya ce goyon bayansa ga Tinubu ya samo asali ne daga irin kokarin da shugaban kasar wajen tunkarar matsalolin da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
- Dangote da BUA za su gurfana a majalisa kan badakalar haraji
- An kama lakcarorin bogi a Jami’ar BUK
- Duk alhajin Najeriya ya samu tallafin N1.6m —NAHCON
A cewar mawakin, samar da Ma’aikatar Kiwo da Hukumar Raya Arewa maso Yamma da kuma ba wa kananan hukumomi ’yancin gashin kansu, an yi su ne domin yakar yunwa da fatara da rashin tsaro a Arewa.
Mawakin ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar cewa ayyukan Shugaba Tinubu za su samar da sakamako mai kyau a cikin watanni uku masu zuwa.
A cewar Rarara, shugaba Tinubu ya cimma muhimman nasarori da shugabannin da suka shude ba za su iya ba.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya musamman na Arewa da su shiga gangamin hadin kai don jinjina wa gudunmawar Tinubu ba Najeriya.
Haka kuma ya shawarci shugabannin kananan hukumomi da su sarrafa kudaden da suke samu daga asusun tarayya yadda ya kamata.