✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurunkus: Sunusi II ya zama Halifan Tijjaniyya a Najeriya

Wata uku ke nan nan ana ta kai ruwa rana kan nada shi a wannan matsayi.

A ranar Litinin da ta gabata ce aka tabbatar da nadin tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin Halifan Tijjaniyya a Najeriya.

Wata uku kafin nan an yi ta kai ruwa rana kan nada shi a wannan matsayi.

Kafafen sadarwar zamani ne suka fara bayar da labarin nadin Halifan tare da yada bidiyon nadin da suka ce sun samo ne daga shafin Facebook na Babban Halifan Tijjaniyya kuma Halifan Sheikh Ibrahim Nyass, wato Sheikh Mahiy Inyass.

Kafafen sun kawo fassarar jawabin da Sheikh Muhammadu Mahiy Nyass ya yi a wajen nadin Halifan a birnin Kaulaha a yayin rufe tafsirin bana.

“Muna sanar da kowa, kuma duk mai kira ya yi kira cewa ma’abocin kullawa da warwarewa da zartarwa a cikin sha’anin Faidhar Tijjaniyya, wanda shi ne Khalifa Sheikh Mahi Inyass, ya nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Halifan Tijjaniyya a Najeriya.

“A bisa wannan zartarwa, muna rokon Ubangiji cikin kankar da kai, Ya karfafe shi bisa daukar wannan nauyi da aka dora masa, kuma ya aiwatar da shi kamar yadda aka yi tsammani ko fiye da haka,” kamar yadda wani mai suna Abubakar Sirrin Baye Inyass ya fassara.

A wani bidiyo da wakilinmu ya ci karo da shi, an nuno Sheikh Mahiy da Malam Sanusi II, inda Sheikh Mahiy yake kwarzanta tsohon Sarkin Kanon da cewa mutum ne mai ilimi da wayewa kuma shugaba daga shugabannin Musulmin Najeriya da cikin taimakon Allah zai iya taimakon addinin Allah ya taimaki Darikar Tijjaniyya, inda ya bayyana nada shi Halifa tare da fatar zai sauke sabuwar amanar da aka dora masa.

Yadda tafiyar ta faro

Tun a watan Agustan bara ne aka fara rade-radin nada Malam Muhammadu Sanusi II a matsayon Halifan Tijjaniyya a Najeriya, inda a ranar 10 ga Agusta Gidauniyar Masoya Muhammadu Sanusi II ta bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne.

Kungiyar ta fadi a wata sanarwa mai taken ‘Khalifanci bai tabbata ba’ da Shugabanta Malam Aminu Dan Almajir ya sanya wa hannu cewa zuwa lokacin wannan magana ba gaskiya ba ce, amma suna fatar haka.

Kwatsam a ranar 13 ga Maris, 2021 sai ga labarin cewa an nada Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin Halifan Tijjaniyya a Najeriya.

Bayanai sun ce an yi nadin ne a wajen taron Maulidin Kasa da aka gudanar a Sakkwato, inda aka ce Sheikh Makki Nyass ne ya nada Sanusi II a matsayin Halifan.

Sai dai kuma Jagoran Darikar Tijjaniyyar, Sheikh Muhammadu Mahiy Nyass ya warware wannan nadi jim kadan bayan sanar da hakan, inda ya ce ba su aiko kowa ya nada Halifan ba.

Sheikh Mahy Nyass, ya tabbatar da cewa su daga can Kaulaha ba su turo kowa ba kan maganar Halifancin Tijjaniyya a Najeriya.

Ya ce abin da aka yi ba haka ya kamata ya zama ba, ya ce a Najeriya akwai manyan shehunai da manyan shugabannin zawiyyoyi da suka kamata a tuntuba, amma ba a yi haka ba.

Takardar shaidan nadin Sarki Sanusi II Khalifa. (Hoto: @MSII_dynasty).

Yadda aka tabbatar min da Halifancin – Sanusi na II

Tsohon Sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi II, ya bayyana yadda aka nada shi a matsayin Halifan Tijjaniyya a Najeriya lokacin da ya kai ziyara Kaulaha a ranar Litinin da ta gabata.

Ya bayyana haka ne a hirarsa da Sashin Hausa na rediyon BBC a ranar Talata, inda ya ce Sheikh Mahy ya turo fitattun malamai zuwa Najeriya su tattauna kan wanda suke so ya jagoranci darikar a Najeriya.

Ya ce kashi 98 cikin 100 na malaman sun zabe shi, “Kamar yadda mutane suka sani wannan matsayi na kakana ne … marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, kuma a daukacin rayuwata ba ni da wani buri da ya wuce in gaje shi.

“Na gaje shi wajen zama Sarkin Kano, kuma a yau Allah Ya sa na samu damar gadonsa a matsayin Halifan Tijjaniyya a Najeriya.

“Babu abin da zan ce sai godiya ga Allah tare da rokonSa Ya jagorance ni wajen sauke nauyin da aka dora mini,” inji shi.

Da yake amsa tambaya kan ko Sheikh Dahiru Bauchi na da masaniya kan tabbatar masa da Halifancin, sai ya ce babu rashin jituwa a tsakaninsa da Shehin Malamin wanda kaka yake gare shi.

“Sheikh Dahiru bai taba fadin mummunan abu game da ni ba, face kauna da goyon baya.

“Shi babana ne kuma babban aminin kakana Sarki Muhammadu Sanusi I,” inji shi.

Ya ce Halifa Mahiy ya turo dan uwansa Sheikh Kuraishi ya zagaya ya tuntubi malamai da mukaddamai da dama don jin ra’ayinsu kuma sun amince.

Ya ce duk da cewa iyalan Nyass sukan zabi wanda suke so ne, amma Babban Halifa yakan bukaci a tuntubi malamai a Najeriya kuma sun zagaya an amince da shi.

Sabon Halifan ya ce a shirye yake ya tunkari kalubalen da darikar ke fuskanta a wannan zamani.

Malam Sanusi II ya ce akwai matsaloli a bangarorin ilimi da aikin yi da hakkin iyali da abubuwan da suka shafi tsangaya da zawiyyowi musamman a Arewacin Najeriya.

Ya ce zai mayar da hankali a wadannan bangarori yadda ’yan darika za su san cewa lallai ana Karni na 21.

Ya ce ’yan darika Musulmi ne, don haka duk wasu matsaloli da sauran Musulmi ke fuskanta a Najeriya su ma suna fuskanta.

Halifan Tijjaniyyar ya ce lokaci ya yi da miliyoyin ’yan darika za su karfafa kansu su yi ilimi mai zurfi yadda za a rika damawa da su a harkokin kasa kuma su bayar da gudunmawarsu ga ci gaban kasar.

Ya ce zai yi amfani da wannan mukami na Halifan Tijjaniya wajen taimaka wa Najeriya game da batun tsaro.

“Darikun sufaye dama mutane ne da kowa ya san su da son zaman lafiya da rokon Allah, ba a samun mutane da suke da tarbiyya irin ta darika sun shiga harkokin ta’addanci,” inji tsohon Sarkin na Kano.

Don haka ya ce za a dukufa rokon Allah don neman sauki a matsalolin tsaro a Najeriya.

Sarki Sanusi na II yanzu ya gaji kakansa Halifan Tijjaniya na farko a Najeriya wato Sarki Muhammadu Sanusi I murabus kuma ya taba cewa ba ya da wani buri a rayuwa da ya wuce hawa kujerar kakansa.

Tun rasuwar marigayi Sheikh Isyaka Rabiu a shekarar 2018 ba a nada Halifan Tijjaniya a Najeriya ba.

Nada Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyya ya zo da ce-ce-ku-ce a Najeriyar inda wasu bangarorin Tijjaniyar suka ce ba su amince da nadin nasa ba.

A farkon wannan mako ne Muhammadu Sanusi II ya kai wata ziyara Kaulaha a kasar Senegal, wadda ita ce cibiyar Darikar Tijjaniyya ta duniya kuma mahaifar Shehu Ibrahim Nyass.

Sheikh Mahi Nyass ne ya tarbe shi kuma ya ayyana shi a matsayin jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya.

Muna jiran bayani daga Kaulaha – Muridai

Wadansu mabiya Darikar Tijjaniyya dai suna ganin fitattun malaman Musuluncin nan Sheikh Dahiru Bauchi da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh a matsayin manyan shugabannin darikar a Najeriya.

Kuma a baya, fadin Malam Sanusi II a matsayin Halifan Tijjaniyya ya haifar da takaddama, tare da nuna cewa ba a bi ka’ida ba.

Haka a wannan karo ma sake nada Malam Sanusi II a matsayin Halifan Tijjaniyya ya sa an rika samun mabambanta ra’ayoyi, wadansu na goyon baya, wadansu na suka.

Misali, shafin Tijjaniya Online, ya fadi a ranar 11 ga Mayun nan cewa: “Ba mu amince da nadin Sanusi Lamido Khalifan Tijjaniya ba, sai dai Khalifan Wahabiyawa,” inda ya jingina hakan ga Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi babban dan Lisanul Faidha, Sautul Islam Sheikh Dahiru Usman Bauchi da sunan isar da sako a madadin Shehin Malamin.

Shafin ya ce Darikar Tijjaniya ba jam’iyyar siyasa ba ce, inda ya ce zuwan Khalifa Mahiy Inyass nan Najeriya an riga an tattauna an daddale a gabansa cewa babu wani abu mai kama da haka a Tijjaniya, inda shafin ya ruwaito cewa, “A iya sanina Gausi ne kawai yake nada Khalifa a Faidha ba wani nadadde ba.

“Sannan wanda aka nada ba cikakken dan Faidha ba ne sojan gonar Wahabiyawa ne domin har yanzu bai daina karantar da littattafansu ba kamar littafin Ibnul Kayyim dalibin Ibn Taimiyya da su Ibnul Jauzy.”

Sannan wasu majiyoyi na almajiran Sheikh Dahiru Bauchi ta ce bangarensu ba ya da wata masaniya kan nada Malam Muhammadu Sanusi a matsayin Khalifan Tijjaniya.

 Majiyoyi masu tushe a Zawiyyar Shehin sun shaida wa Aminiya cewa baban dan Shehu Dahiru, Sayyadi Ibrahim Sheikh ne Shehu Mahiy ya nada a matsayin mai magana da yawunsa a Najeriya kuma bai fada musu wannan batu ba har zuwa lokacin da ya bar Bauchi don zuwa Umara a ranar Talata.

Sun ce kuma bangaren mutanen Kaulaha ba su tuntubi Shehin ba kamar yadda Halifa Mahy ya yi alkawari cewa in akwai bukatar za a yi, tilas sai an zauna da malamai.

“Ba a zauna da malaman ba tukuna, ba mu da wani labari kan wannan batu,” inji daya daga cikin majiyoyin.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Sheikh Dahiru Bauchi ko Sayyadi Ibrahim ya ci tura domin tunda Shehin ya koma Bauchi daga Tafsirin da ya gudanar a Kaduna bai fita waje, in baya ga shekaranjiya da ya fita Sallar Idi.

Sai dai wata majiya ta ce an cimma matsaya a bangaren Shehin cewa kada wani ya yi magana a kan abin da ba a san kansa ba, domin Shehu Mahy yana iya nada Halifansa na kansa a ko’ina, don haka a jira a samu cikakken bayanin abin da ya faru.

Majiyar ta ce, idan aka ga takardar da aka rubuta ne za a iya sanin bayanin da za a yi, don kauce wa yin kuskure.

Darikar Tijjaniya dai ta samo assali daga Arewacin Afirka inda ta yadu a Afirka ta Yamma musamman kasashen Senegal da Gambiya da Mauritaniya da Mali da Guinea da Nijar da Chadi da Ghana da Najeriya da kuma Sudan.