Ta tabbata tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Ogbia ta 13 da Jonathan ya fito a Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa ne suka tabbatar cewa tun da dadewa tsohon shugaban kasar ya yi rajista da jami’yyar.
2023: Dalilin da gwamnonin Arewa ke son Jonathan ya dawo
- Takarar 2023: Buhari ya umarci Gwamnan CBN ya ajiye aiki
- 2023: PDP ta jingine karba-karba a kujerar shugaban kasa
Shugaban APC na mazabar Ogbia ta 13, Igori Freedom, ya ce, “Ina da cikakkiyar masaniya cewa an yi wa Jonathan rajista a APC, duk da cewa yin rajista ba abu ne da dole sai an yayata ba.
“A lokacin da ya yanki katin, rajistar na hannuna, kuma a lokacin shi da wasu kusoshin PDP ne da suka dawo APC, bayan nasarar dan takarar jam’iyyar, David Lyon a zaben gwamnan da aka gudanar a 2019.
“Kana iya zuwa ka tambayi shugaban APC na jiha, ka fada mishi cewa shugaban gunduma ya yi amanna cewa tsohon shugaban kasar ya yi rajista a matsayin dan jam’iyya.
“Yanzu an riga an gama aikin rajista, ba zan iya ba ka alkaluman komai ba, saboda na riga na mayar musu da duk alkaluma da bayanan da ke wurina.
“Idan ka samu shugaban jam’iyya na jiha, Cif Dennis Otiotio, zai yi maka karin bayani.” inji shi.
‘Ban sa da Jonathan a APC ba’
Sai dai kuma wakilinmu ya yi tuntubi Shugaban APC reshen Jihar Bayelsa, Barista Dennis Otiotio, amma ya ce ba shi da masaniyar rajistar Jonathan jam’iyyar.
Ya shaida wa wakilin namu cewa: “Abin da ya kamata shi ne ku kira hedikwatar jam’iyya ta kasa, domin sanin hakikanin halin da ake ciki.
“Mu dai a nan sakatariyar jiha ba mu da masaniya ko wani bayani game da dawowarsa jam’iyyarmu.”
Dambarwar takarar Jonathan
A farkon makon nan ne dai kura ta turnike bayan wata kungiyar Fulani ta saya wa tsohon shugaban kasar fom din takarar shugaban kasa a inuwar APC a zaben 2023.
Daga bisani dai ya fito, ta bakin kakakinsa, Ikechukwu Eze, ya nesanta kansa da kungiyar da fom din da ta saya mishi a kan Naira miliyan 100.
A cewarsa, hasali ma shi ba dan jam’iyyar APC ba ne.
Idan ba a manta ba mun kawo rahoto game da wani wani tsohon gwamna yana cewa wasu gwamnonin jam’iyyar APC biyu ne suke jagorantar tafiyar Jonathan din, kuma sun tallata shi ga Fadar Shugaban Kasa.
“Su (an sakaya sunayensu) ne suke tallata tafiyar Jonathan domin su taka wa Bola Tinubu burki, bayan sun lura cewa mataimakin shugaban kasa ba shi da karfin karawa da Tinubu,” inji tsohon gwamnan.
Mutane da dama dai sun saki baki da jin cewa an saya wa tsohon shugaban kasar fom din takarar komawa kan kujerar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC.
Majiyoyinmu sun shaida mana cewa wasu gwamnoni masu ci daga yankin Arewa, kuma na hannun daman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne suka saya wa Jonathan fom din.
Tsohon gwamnan ya ce, “Suna da nasu manufar; mutumin da wa’adin mulki daya kawai zai yi suke so, kuma suna so ya dauke su a matsayin mataimakin shugaban kasa”.
Buhari ne kan gaba
“Babban magoyin bayansa shi ne Shugaban Kasa, kana ganin zai fara tunanin yin hakan in ba tare da ya samu goyon bayan ‘Baba’ ba?
“Bai fito fili ya fada ba cewa yana so; Ana son ya fito ne saboda an fi nutsuwa da shi ya zama magajin Buhari,” inji majiyar.
Jonathan zai koma APC
Idan ba a manta ba, a watan Afrilu ne tsohon Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar APC Reshen Jihar Bayelsa, Diekivie Ikiogha, ya ce saura kiris tsohon shugaban kasar ya fice daga PDP.
“Zai bayyana ne bisa gayyatar da APC ta yi mishi na ya fito, kuma yana nazari a kai; an riga an gama abubuwa da yawa, ana ci gaba da tattauanwa kuma za a gayyace shi.
“Muna kokarin shawo kansa kuma ina ganin zai amsa kiran, idan komai ya daidaita kuma zai tsaya takara,” a cewarsa.
Yana da ’yancin fitowa
Wani mai sharhi kan al’amura, David West, ya ce duk da cewa a baya tsohon shugaban ya sanar cewa ya daina siyasar jam’iyya, yana da ’yancin tsayawa takarar kowace kujera a Najeriya.
Amma ya ce da wuya Jonathan ya tabuka wani abu fiye da yadda aka gani a lokacin mulkinsa na farko.
“Na san idan aka ba shi mulkin Najeriya, shekara hudu rak zai yi, akasin hakan kuma zai haifar da da rikici.”
Dalilin saya wa Jonathan fom?
“Majiyoyi da dama masu kusanci da lamarin sun bayyana cewa gwamnonin biyu, wadanda na hannun daman Shugaba Buhari ne, sun ja ra’ayin wani bangare na Fadar Shugaban Kasa domin cim ma manufarsu ta shigar tsohon shugaban kasar takarar shugaban kasa.
“Majiyoyin sun kuma bayyana wa wakilanmu sunan gwamnonin da ke wannan yunkuri, amma muka ba mu bayyana su ba, kasancewar ba mu samu jin ta bakinsu ba zuwa lokacin hada wannan rahoton, sun yi tafiya kasar waje.
“Daya gwamna ya fito ne daga Arewa maso Yamma, dayan kuma daga Arewa maso Gabas, kuma tun shekarar da ta gabata suka fara wannan yunkuri, amma daga baya suka jingine shi domin tallata takarar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
“Amma da gwamnonin suka ga takarar Emefiele ba ta samu karbuwa sosai ba, sai suka koma kan shirinsu na Jonathan.
“Gwamnonin suna taka muhimmiyar rawa a jam’iyyar APC a cikin ’yan shekarun nan.
“Shi kansa Jonathan daga take-takensa ya nuna yana ra’ayin hakan,” inji rahoton na Daily Trust.
Ku jira ku gani, inji Jonathan
A baya tsohon shguaban ya ce wa masu kiraye-kirayen ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023 cewa, “Ku jira ku gani.”
Hakan ta sa ake ganin yana nazari ne kafin ya bayyana ra’ayinsa da kuma jam’iyyar da zai fito takarar a inuwarta.
A babban zaben 2015 ne dai Shugaba Jonathan na jam’iyyar PDP, a lokacin, ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar adawa ta APC, Muhammadu Buhari, wanda ya kawo karshen shekara 16 da PDP ta yi a jere tana mulkin Najeriya, tun daga 1999.
Sai dai a tsawon shekara shida da suka gabata, ba a ganin shi a tarukan PDP.
A hannu guda kuma alakarsa da Shugaba Buhari da manyan kusoshin jam’iyyar APC na kara karfi, lamarin da wasu kusoshin jam’iyyar adawar ba su yi na’am da shi ba.
Jonathan ba dan APC ba ne
Amma a lokacin, Shugaban Jam’iyyar APC Reshen Jihar Bayelsa, mahaifar Jonahta, Dokta Dennis Otiotio, ya ce har yanzu tsohon shugaban kasa bai shiga jam’iyyar ba.
Amma ya bayyana cewa duk da haka Jonathan din na da ’yancin shigar ta a duk lokacin da ya ga dama.
Dennis ya bayyana hakan ne a ranar Talata kan yunkurin masu son ganin tsohon shugaban kasar ya fito takara a APC a zaben 2023.
Ya ce, “Har yaznu tsohon shugaban kasar bai yi rajista da APC ba, amma yana da ’yancin yin haka, kuma shirye muke mu karbe shi.
“A matsayinmu na jam’iyya, babban burinmu shi ne mu lashe zabe, kuma hanyar da za mu iya yin hakan cikin sauki kawai ita ce ta karbar karin mutane a cikinmu,” inji Dokta Dennis.