Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima ya samu kuri’a hudu a zaben zaben fid-da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC.
An sanar da kuri’ar tasa ne bayan an kammala tantance kuri’un da daliget sama da 2,000 suka jefa a zaben na ranar Laraba.
- Kuri’a 1 Ministan Ilimi ya samu a zaben dan takarar shugaban kasa
- Tsakanin Tinubu da Osinbajo za a kara a zaben dan takarar APC —Kabiru Gaya
- Rikici ya barke tsakanin shugaban APC na Jihar Kano da jami’an tsaro a taron APC
Bayan zaben wanda ya gudana a dandalin Eagles Square da ke Abuja, tsohon Minista a Ma’aikatar Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya samu kuri’a daya.
Tsohon Gwamnan Jihar Imo, da tsohon wanda ya yi
Kuri’un da ‘yan takarar suka samu zuwa yanzu su ne:
- Chubuike Rotimi Amaechi, tsohon Ministan Sufuri – 316
- Farfesa Yemi Osinbajo, Matamakin Shugaban Kasa, – 235
- Sanata Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa – 152
- Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi – 47
- David Umahi, Gwamnan Jihar Ebonyi – 38
- Ben Ayade, Gwamnan Jiyar Kuro Riba – 37
- Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani Yerima – 4
- Chukwuemeka Nwajiuba, tsohom Minista a Ma’aikatar Ilimi – 1
- Dokta Christopher Onu – 1
- Sanara Rochas Okorocha, tsohon Gwamman Jihar Imo – 0
- Fasto Tunde Bakare, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa – 0
- Tien Jack-Rich – 0
- Abasi Ikoli – 0