✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurame da makafin Bauchi na bukatar alawus

Haba Gwamnatin Bauchi ki tausaya wa kurame da makafi, wadanda suke karatu a Cibiyar Karatun Musamman (Special Education Centre Bauchi) a mayar musu da alawus…

Haba Gwamnatin Bauchi ki tausaya wa kurame da makafi, wadanda suke karatu a Cibiyar Karatun Musamman (Special Education Centre Bauchi) a mayar musu da alawus dinsu na wata-wata da aka daina iyanmu. Wannan zai sa su samu natsuwa wurin yin karatu, ba tare da sun fita yawon barace-barace ba. Daga Illiyasu Wakili Akuyam Turakin Kuramen Misau 08032757733.

Sakonnin waya

Ga Bamanga da Goodluck

Salam Edita, a mika min sakona. Bamanga da Goodluck su gane cewa wannan mulkin farar hula ne, ba na soja ba. Amaechi Allah Ya kara muku kwarin gwiwa. Daga Bashiru Aliyu Yalwan Shandam. 07161191204.

Yakawada an bar baya da kura
Salam Aminiya kun kawo rahoton abin da ya faru a garin Yakawada, kun bar baya da kura. Don kuwa an kakkama mutane da yawa, tunda abin ya faru ana tsare da su ba beli. Kuma wani tsohon Sakataren Gwamnatin Kaduna,  yasa ake yi wa jama’a, wasu ma saboda siyasa. Daga Musa Adam Mile 12 08107970874.

Sabuwar PDP a koma APC
Aminiya gaskiya muna godiya. Bayan haka ya ’yan sabuwar PDP, idan don talaka kuke yi, to ku hade da APC, don kafa mulki mai adalci, inda babu bambanci tsakanin talaka da mai kudi a 2015. Daga 08153621801.

Ga Sarkin Gumel
Assalamu alaikum. Edita ka mik amin gaisuwa da taya murnar cika shekara 33 ga Maimartaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Mai Lautai. Alah Ya kara lafiya. Daga dan Ganji 07066457260.

Ga Gwamnati da Malaman Jami’o’i
Salam Aminiya. Don Alah ku yi kira ga Gwamnatin Tarayya da malaman jami’o’i da su yi hakuri, su daidaita, domin dalibai su samu damar ci gaba da karatunsu. Daga Isma’il Alkyaba Funtuwa 07039495283.

Ga Mahajjatan bana
Assalamu alaikum. Don Allah Edita ka mika min gaisuwata ga mahajjatan bana. Allah Yasa a sauke lafiya. Mu ma Allah Ya sa wata rana mu je. Amin. Daga 08162209074.

Godiya Sule Lamido
Edita ka bani dama in mika godiya ga Gwamnan Talakawa Sule Lamido,a kan gyaran hanya da aka fara, daga Kazaure zuwa Roni. Allah Ya saka da alherinsa. Mun gode. Daga Sani I. Roni 07069744327.

Ga ’yan majalisa
Ku tattauna tsakaninku game da yiwuwar raba Najeriya, ba tare da an yi yaki ba. In an yarda a rabu, to shi ke nan, sai a nada kwamiti don ya saurari shawarwari daga jama’a. Halin da ake ciki a yanzu gara kow aya kama gabansa. Daga Y. Sani Sakkwato 08068322646.

Kwankwasiya a White House
Mu Kanawa muna tare da Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, duniya ta yarda da shugabancinsa; White-house ma akwai ’yan kwankwasiyya. Muna nan a PDP har sai mun tarwatsata. Daga Abdulkadir Abba Suleman dangoro 08093553628.

Ga sabuwar PDP
Aminiya ku gaya wa ’yan majalisa da gwamnoni bakwai masu sabuwar PDP idan kuka tsaya kan manufarku, b aku sorata ba, to kowa ya koma amzabarsa zai sake cin zabe, saboda kun yi farin jini a urin talakawan Arewa. Daga Majidadin Doho, Jihar Gombe 08080329916.

Ga Gwamnatin Najeriya
Gaskiya ya kamata gwamnati  akama Asari Dokubo, don ya fadi dalilinsa na fadin haka a 2015 za a zubar da jini. Daga dankasa Nagari Mutawakil A kankara 07032154483.

Ga korarrun ministoci
To kurarrun ministocin Najeriya me kuma za ku ce da al’ummarku tunda ba ku tsinana mana komai ba. Daga Sulaiman SBK 07038999155.

Ga Muhammadu Buhari
Aminiya ina so a mika min jinjina ga shugaban talakawan Najeriya, Janar Muhammadu Buhari da hakurin da yake yi wajen tabbatar da gaskiya da adalci a Najeriya. Baba muna nan ba gudu, ba ja da baya. 2015 Allah Ya taimake mu, amin. Daga Alyasa’u Haruna Imam Ningi, Jihar Bauchi. 08058824152.

Shugabanni nagari
Assalamu alaikum. Aminiya, mu dai fatanmu, Alah Ya ba mu shugabanni maso sonmu, ba wanda muke so  ba, a kasata Najeriya. Daga Yunusa Saleh Fago, Daura, Jihar Katsina 07036880005.

Ga masoya Aminiya
Edita sannu da aiki, don Allah ka ba ni dama in mika sakon gaisuwa ga duk masu amfani da jaridar Aminiya, a duk inda suke a fadin duniya. Da fatan Allah Ya kara daukakata. Daga Badamasi Aliyu Rijiyar Lemo, Kano, 08039552160.

Aminiya a kara filin sakonni
Aminiya na gani, na gode, Allah Ya biya. Amin. Don Allah ku kara wa shafin sakonninku fili. Nagode Daga Idris Yaro Abuja 07061860202.

Jinjina ga Aminiya
Jinjin mai karfi ga ma’aikatan Aminiya. Amincin Allah Ya kara muku basira, ya kara daukaka ku, ya raba ku da sharrin mahassada. Daga Azzubair M. Fagge Kano 08034412272.

Ga Gwamnan Kaduna
Don Allah Aminiya ki isar min da sako a Gwamnan Kaduna, bana jin ana yabonsa, a ko ina. Daga Hauwa karamar Hukumar Jama’a, Jihar Kaduna 08034906426.

Ga Hukumar SSS
Edita ka ba ni dama in yi kira a Hukumar Tsaron ta Farin Kaya, da ta rika bin doka a kasar nan. Daga Muhammad Isa (Dogon jeji).

Muna goyon bayan Kwankwaso
Salam Aminiya don Allah ki isar min da sakona zuwa ga Kwankwaso, muna goyon bayanku a kan sabuwar jam’iyar PDP. Daga Ali NCC Money 08033096609.

Ga Masoyan Buhari
Aminiya ba ku son mika min gaisuwa ga masoyan Buhari, wato sakatare na masu sayar da waya na Jihar Sakkwato da Agent Yahaya dan Madami. Jamar Sakkwato da Najeriya APC na nan 2015. Daga Rilly dan Yabo Communication, Sakkwato. 08066227322

Ga Bamanga Tukur
Edita ka yi hakuri ka isar da sakona ga Bamanga Tukur, da yake mamakin kashi 25 cikin 100 na samun nasara kan kashi 75 cikin 100. Ai karfin ba na su ba ne, na Allah ne. Ko baya ganin misalin da Allah Ya buga ba ne cikin Suratul An’am aya ta 64 zuwa 66 ba ne? Allah Ya shiryar da azzaluman shugabanni. Idan kuma ba za su shiryu ba, Allah ya dora kashi daya cikin 100 a kan 99 cikin 100, ba 25 ba. Daga Sadi Sani Rurum Rano. 07060831104.