✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurakuran kwalliya wadanda ba a san ana aikata su ba

Akwai kurakurai da dama wadanda mata suke yi wajen kwalliya, ba tare da sanin hakan kuskure ba ne. Ya kamata a kiyaye idan an zo…

Akwai kurakurai da dama wadanda mata suke yi wajen kwalliya, ba tare da sanin hakan kuskure ba ne. Ya kamata a kiyaye idan an zo shafa kayan kwalliya a fuska, musamman wajen sanya gazal da hodar fandesho da janbaki da sauran kayan kwalliya, wadanda ba su dace da kalar fatar mutum ba. A yau na lissafo irin kurakuran da mata suke yi wajen kwalliya. In ko ba a gyara ba, sai a ga mutum yana kama da dodo.

·         Shafa hodar fandesho da ba ta dace da fatar mace ba. Sau da yawa sai a ga mace ta yi kwalliya da hodar fandesho da ba ta dace da kalar fatarta ba. Ya kamata a sami kalar fandesho da ta dace da kalar fatar mace, kafin a yi amfani da shi.

·         Shafa kayan kwalliya a fuska mai gautsi. Idan aka shafa kayan kwalliya a fuska ba tare da shafa wa fuskar mai kadan ba, lallai kwalliyar ba za ta yi kyau ba. Man jiki ko na fuska na gyara fata saboda haka, ya kamata a rika shafa man fuska kafin shafa hoda.

·         Idan kina da labba manya, bai kamata ki  bi labbanki da gazal ba. Domin yin hakan na kara fitar da girman labbanki. Amma idan ke mai kananan labba ce, za ki iya bin labbanki da gazal din baki (lip liner).

·         Amfanin gazal a gira. Idan ke mai cikakkiyar gira ce, bai kamata ki dada wani gazal a kan girarki ba. Sai dai idan ke ba mai cikakkiyar gira ba ce, za ki iya cika girarki da gazal, wanda kalarsa daidai take da gashin girarki.