Abin da ya kamata jagororin Arewa su mayar da hankali a kai shi ne hanyoyin da za a bi domin yankin ya amfana da mulkin Tinubu.
Jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Alhaji Musa Ilyasu Kwankwaso, ya shawarci ya shawarci dattawan Arewa su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da gwamnoni da kuma fadar shugaban kasa domin ganin yankin ya ci moriyar dimokuraɗiyya.
A cewarsa, “Masu shiga kafofin sada zumunta suna cin mutuncin shugabanni suna yi wa al’umma illa ne kawai da yaudarar jama’a.
“A cikin shekara daya da ya yi yana mulki ya samu nasarori da dama amma wasu sun rufe idanunsu kan nasarorin da gwamnatin tasamu,” in ji shi.
Ya bayyana cewa, maimakon su rika yada labaran karya da zarge-zarge marasa kan gado, ya kamata su yi kira da a yi abin da ya dace a yankin.
“Ya kamata su fito su yi kira da a kammala aikin titin Abuja zuwa Kano, da aikin layin dogo zuwa ƙasar Nijar da aikin bututun iskar gas na AKK da aikin wutar lantarki ta Mambila.
“Su riƙa yin rubuce-rubuce da kiraye-kiraye kan batun aikin haƙar mai na Bauchi da Gombe da sauran su, ba wai su riƙa cin dunduiniyar juna ba.”
Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi wannan kira ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashin-tashina kan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje da kuma ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle.
Ya soki zanga-zangar adawa da Matawalle Ganduje da sauran jiga-jigan jam’iyyar, a matsayin wani mummunan yunkuri na cisguna wa Shugaba Tinubu.