✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kura-kuren da mata ke yi lokacin kwalliya

Mata kan tsinci kansu cikin kura-kurai lokacin da suke yin kwalliya ba tare da sun fahimci hakan ba. Don haka ne a wannan mako na…

Mata kan tsinci kansu cikin kura-kurai lokacin da suke yin kwalliya ba tare da sun fahimci hakan ba. Don haka ne a wannan mako na yi muku guzurin bayani don kauce wa kura-kurai yayin kwalliya.
1 A lokuta da dama wasu matan kan dambara hoda ko gazal ko jagira da dai sauransu. Dokar kwalliya ta tanadar idan har an sanya mascara ko hodar eye-shadow ko gazal ko jagira da yawa, to sai a sanya jan baki marar duhu. Kana idan aka sanya jan-baki mai duhu a lebba, sai a sanya eye shadow ko mascara marar duhu. Dambara su da yawa yakan sanya kwalliyar ta zama wata aba daban. Ba wai ba za a sanya jan-baki da kuma sanya hoda a idanu ba ne, a’a, abin da ake nufi idan a wani waje aka sanya mai duhu, to a daya wajen sai a sanya marar duhu.
2 Yayin shafa jan-baki wasu matan kan yi sake har ya taba hakoransu, ko su rika shafawa a kan lebbansu da yake a bushe, yin hakan zai sanya kwalliyar ta zama wata iri. Idan ana so jan-baki ya yi kyawu, ya kuma kayatar, to hanya ta farko ita ce, lebba su zamanto da damshi, wato ba a bushe ba. Kafin a kai ga shafa jan-baki yana da kyawu a shafa man da yake saka damshin lebe. Bayan an shafa jan-baki yana da kyawu a yi amfani da wani kyalle mai tsafta wajen goge wurin da ya yi yawa, domin daidaita yawan jan-baki a lebba.
 3 Yawanci mata sukan yi kuskure yayin da suke shafa hodar ‘cakey foundation’, maimakon ta fito da kwalliya sai ta bata ta. Kafin a kai ga sanya hoda a fuska yana da kyau a rika amfani da sinadaran cleanser don kashe kurajen fuska da kuma fitar da matattun kwayoyin halitta, wanda hakan zai sanya kwalliya ta fito sosai.
4 Yayin sanya hodar eye-shadow wasu matan kan sanya ta wuce misali, har ya zamanto ta fito bau, ko a maka a kwarin idanu, sai ya zama hodar da take fuska ta zama daban, haka ta kwarin idanu ma ta zama wata daban.
5 Yayin shafa hoda wadansu matan kan fara daga kan kumatu ne, wanda hakan yake sanyawa a samu bambancin yawan hoda a fuska, wanda hakan ya kawo a yi goge-goge. Yayin shafa hoda ana so a fara daga goshin ne, sannan a taho zuwa haba. Bayan haka yana da kyawu a rika amfani da faffadan soso wajen shafa hoda don ya rage yawan tabbare-tabbaren da za a rika samu.