✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kura-kuran da ake tafkawa wajen kwalliya

Barkanmu da sabuwar shekara  tare da fatan za a kokarta wajen  gane sirrin kwalliya da kimtsin da ya dace da kowace irin mace da kuma…

Barkanmu da sabuwar shekara  tare da fatan za a kokarta wajen  gane sirrin kwalliya da kimtsin da ya dace da kowace irin mace da kuma sanin irin kwalliyar da ta dace da launinta. A yau na kawo muku kurakuran da ake tafkawa wajen yin kwalliya. Wannan al’amari na jawo matsala, shi ya sa na kawo yadda za a magance wadannan matsalolin.
Mata da dama suna yawaita tafka wadannan kura-kurain ba tare da sanin hadarin da ke tattare da su ba. Da fatan za a kula bayan an gama karanta wadannan sharudda.
• Kada a kwanta barci ba tare da wanke fuska ba; lallai da kwai gajiya da kulawa da irin wadannan matsalar, amma sai mutum ya dage sosai. Datti da kuma maikon fuska na haifar da fesowar kuraje daga fuska. Don haka sai a kiyaye. A rika wanke fuska kullum kafin a kwanta barci.
• A dage da yawan yin dilke a fuska kamar sau biyu a mako. Yin hakan na cire matattun fatar fuska da ba su da wani amfani, kuma da dada wa fuskar haske. Dilke na da matukar muhimmanci a jiki, domin yana dada wa fuskar haske da kuma sheki. Shi ya sa ake yawan gaya wa sababbin amare da su dage da yin dilke.
• A dage da wanke su kayan kwalliya kamar su soson hoda da na gira da sauran su. Idan ba a wanke su, dauda za ta zauna a ciki. Ta yaya kuma za a sanya wa fuskar da aka wanke datti. Sai a kula domin yin hakan na haifar da cututtukan fuska.
• A dage da shafa mai a fuska kafin a yi kwalliya. Yin hakan na rage shekarun mace. Kuma duk fuskar da ba a shafa mata mai ba aka yi kwalliya lallai za a ga kwalliyar ba ta zauna ba.
• A rika wanke fuska a kalla sau biyu a rana. Idan an kasance masu yawan sanya kayan kwalliya, dole ne a na wanke fuska sau biyu a rana, domin idan kayan kwalliyar suka dade a fuska, za a iya samun kurajen fuska.