✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kunguyar ‘yan Arewa ta samu nasara a shekara biyu – Shugaban Otto

Shugaban ƙungiyar ’yan Arewa mazauna unguwar Otto da ke cikin garin Legas Alhaji Bala Muhammad Shu’aibu ya shaida wa Aminiya cewa al’ummar Arewa mazauna yankin…

Shugaban ƙungiyar ’yan Arewa mazauna unguwar Otto da ke cikin garin Legas Alhaji Bala Muhammad Shu’aibu ya shaida wa Aminiya cewa al’ummar Arewa mazauna yankin sun kafa ƙungiyar ta Otto ne domin taimakon kai da kai tare da samar wa al’ummar yankin ci gaba da ba da tallafi ga ma buƙata.

Shugaban ƙungiyar ya shaida haka ne a yayin gudanar da bikin cikar ƙungiyar shekara biyu da kafuwa. Ya ce tun da farko an kafa ƙungiyar ne da mutum 10 a ranar 24/10/2015, bisa manufofin ƙungiyar na haɗa kan al’ummar Arewa mazauna yankin, tare da samar masu ci gaba da taimakon juna.

“Akwai mata zawarawa da mazajensu suka mutu suka bar su da yara marayu. Yana daga cikin manufar ƙungiyarmu na tallafa masu tare da ɗaukar nauyin karatun ’ya’yansu. Sannan muna yin aikin gayya, inda muke yin gyara a masallatanmu da maƙabartu. Yanzu haka muna shirin sayen motar ɗaukar gawa da ɗaukar marasa lafiya zuwa asibiti,” inji shi.

Ya ƙara da cewa sun shirya bikin cikar ƙungiyar shekara 2 da kafuwa ne domin bayyana wa al’umma irin nasarorin da ƙungiyar Otto ta samu tun bayan kafuwarta tare da faɗaɗa ƙungiyar zuwa sassa daban-daban na Jihar Legas. Ya ce lokaci ya yi da al’ummar Arewa mazauna jihar ya kamata su haɗa kansu domin samar wa kansu ci gaba mai ɗorewa.