✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyramu za ta rika ciyar da almajirai 1000 a Jos – Imam Bukhari

Imam Bukhari Ben Ishak Al-Bayaneey shi ne Shugaban Kungiyar Ciyar da Almajirai ta Al-Wifak Almajiri Food Support Programme da ke Jos a Jihar Filato, a…

Imam Bukhari Ben Ishak Al-Bayaneey shi ne Shugaban Kungiyar Ciyar da Almajirai ta Al-Wifak Almajiri Food Support Programme da ke Jos a Jihar Filato, a tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya ce kungiyar za ta rika ciyar da almajirai masu karatun Alkur’ani 1000 a garin Jos ta hanyar ba su abinci da tufafi da magunguna da sabulai:

 

Me ya karkafa muku gwiwar kafa wannan kungiya?

Wannan kungiya wadansu matasa ne suka hadu suka kafa ta a nan garin Jos. Kuma manufar kafa kungiyar ita ce tallafa wa almajirai masu karatun Alkur’ani da suke barace-barace. Muna da burin mu taimaka wajen inganta tsarin almajiranci  ta hanyar tallafa musu da abinci mai kyau da sutura da magani da man shafawa da sabulai, don ganin sun daina barace-barace.

Har ila yau manufar wannan kungiya ce ta taimaka wa matan da mazansu suka rasu suka bar marayu da  taimaka wa matasa wajen samar musu ayyukan yi.  Wadannan su ne manufofin wannan kungiya.

Kamar yaya kuke yi wajen gudanar da ayyukanku?

Mun dauki tsari ne guda biyu wajen gudanar da ayyukanmu. Da farko mun fara horar da matan da za su rika dafa wa almajaran abinci. Wadanda su ne za su rika dafa abincin tare da raba wa almajiran. Muna son kowace mace mai dafa abinci daya,  ta rika dafa wa almajirai 10, abinci.

Kuma a wannan tsari mun shirya za mu fara da ciyar da almajirai1000, a nan Jos. Kuma mun shirya za mu rika bai wa masu dafa abincin, abincin da za su rika dafa wa wadannan almajirai. Akwai katinmu na almajiri da za mu raba wa almajiran da za mu rika ba su abincin. Za mu yi zama da shugabannin tsangayu na Jihar Filato, don gano yawan tsangayu da almajiran da muke da su a nan Jos don gudanar da wannan aiki.

Wannan  nan aiki namu ba zai tsaya ga Jihar Filato kadai ba, muna da burin ganin mun fadada shi zuwa jihohin da suke da almajirai masu barace-barace a kasar nan.

Bayan almajirai sai marayu, kamar yadda za mu rika tallafa wa almajirai da abinci, haka za mu rika tallafa wa marayu da abinci, a nan Jihar Filato.

Yaya ka ga yadda al’umma suka karbi ayyukanku zuwa yanzu?

To mun gode Allah kan  yadda jama’a da sauran wadanda ayyukanmu suka shafe su, suka fahimce mu. Domin duk kyan abin da ka zo da shi, idan jama’a ba su  fahimce ka ba, abin ba zai yi tasiri ba. Musamman wannan abu da muka zo da shi, na zamani. Wanda  yawaici ana ganin almajirai kamar mutane ne da ba su da irin wannan tunani. Amma abin mamaki, sai suka ba mu hadin kai, suka fahimci cewa ba muna son mu kau da su daga karatun Alkur’ani da suke yi ne ba. Muna son mu kara inganta karatun Alkur’ani ne, mu inganta mutuncin masu karatun a rika daukarsu da kima, kamar yadda gwamnati take daukar  wadanda suke karatun boko. Babu shakka mun samu goyon baya daga kowane bangare na al’umma, kamar malaman addini da kungiyoyi da ’yan jarida. Wannan babban abin farin ciki ne.

Wadanne hanyoyi kuke bi don samun kudin gudanar da ayyukanku?

Babu shakka a wannan zamani babu abin da zai iya yiwuwa sai da kudi. Don haka a wannan kungiya cikin abin da Allah Ya huwace mana, muke samu muke gudanar da ayyukanmu. Muna tara taro da sisi ne, amma muna bukatar wadanda suka yi sha’awar ayyukan da muke gudanarwa, musamman masu hannu da shuni, su zo su tallafa mana domin mu dada samun karfin gwiwar, ci gaba da gudanar da ayyukan da muka sanya a gaba. Muna bukatar a tallafa mana da abinci ko magani da sabulai da sauransu.

Mene ne babban burinku?

Babban burinmu shi ne mu ga almajiranmu sun zamanto yara kamar kowa, ta yadda su ma za a rika daukarsu a matsayin masu karatun ilimi. Burinmu shi ne a gane cewa wadannan almajirai da muke da su a kasar nan, yara ne kamar kowa.

A kiyasin da ake bayarwa a kasar nan, an nuna cewa akwai yara almajirai miliyan bakwai da suke yawo kan hanyoyin kasar nan babu kulawa, wannan babbar matsala ce.

Ganin ayyukan kungiyar ya danganci inganta almajiranci, me za ka ce kan matakin da gwamnati ke shirin dauka, na hana almajiranci a kasar nan?

Wato hana barace-barace a kasar nan, abu ne mai kyau a wani bangaren. Ta wani bangaren kuma yana bukatar a yi nazari sosai kan haka. Tun farko ya kamata mu yi tunani, kan me ya kamata a yi kan wannan al’amari na barace-barace.

Domin idan aka ce za a hana bara, me ake nufi shin za a hana bara ne kwata-kwata, kowa ya je ya zauna ko yaya za a yi? Idan gwamnati ta ce za ta inganta tsarin karatun allo ne, kafin ta hana babu damuwa. Domin idan za a rika bai wa almajirai  wurin kwana da abinci da ruwa, babu wanda zai damu, don an hana bara.

Amma magana ta gaskiya gwamnati kadai, ba za ta iya magance wannan matsala ba, ba tare da ta ji ta bakin malaman makarantun allo ba. Dole ne ta zauna da su ta ji koke-kokensu, ta ji me fahimtarsu, ta ji shawarwarinsu kan wannan al’amari. Kamar a gwamnatin da ta gabata ta tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ta fito da tsarin inganta makarantun allo a kasar nan, amma tsarin ba a bi ta inda ya kamata ba. Domin a lokacin, maimakon a gyara makarantun tsangayu na allo da suke cikin gari sai aka tafi bayan gari, can lungu inda babu kowa aka gina makarantun allo. Wannan tsari ya nuna cewa kamar ana kyamarsu ne, don haka bari a kwashe su, daga cikin gari a kai su waje a ajiye. Ka ga wannan ba za a fahimci, gwamnati ba.

Wane kira za ka yi ga al’umma game da muhimmancin tallafa wa tsarin karatun allo?

Da farko muna kira ga al’ummar Musulmi da wannan al’amari ya fi shafa. Ya kamata mu gane cewa ba mu da abin da ya  kai Alkur’ani Mai girma, domin shi ne shiryarmu a duniya da Lahira. Don haka ya zama wajibi ga al’ummar Musulmi, kowa ya sanya hannunsa ya bayar da gudunmawarsa ta dukiya ce ko ta basira ce, wajen  inganta karatun Alkur’ani a kasar nan.

Haka gwamnati ta fahimci cewa yaran nan ’yan Najeriya ne kamar kowa, don haka kamar yadda ake ware kudi a bangaren wasanni da bangaren mata da bangaren mawaka da makada, haka wadannan almajirai ya kamata a rika ware musu kudi don kula da su.