✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyoyin JNI da CAN sun yi tir da kashe-kashe a Kaduna

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) da takwararta ta Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Kudancin Kaduna sun yi tir da tashe-tashen hankulan da suka faru a…

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) da takwararta ta Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Kudancin Kaduna sun yi tir da tashe-tashen hankulan da suka faru a garin Kasuwan Magani da ke Karamar Hukumar Kajuru wanda daga baya ya fantsama zuwa wasu sassa a cikin garin Kaduna.

A cikin wata takarda da suka raba wa manema labarai a garin Kafanchan a ranar Talatar da ta gabata,  kungiyoyin biyu da Fasto Michael Maikarfi na CAN da Alhaji Iliya Musa na JNI suka sanya wa hannu, sun yi kira ga mabiya addinan biyu su guji duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali ta hanyar rungumar tattaunawa da nisantar jita-jita.

Kungiyoyin sun bayyana takaicinsu kan yadda matafiya da sauran jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba ke fadawa tarkon fusatattu a duk lokacin da wani abu ke faruwa a wani sashi, inda suka yi kakkausar suka ga masu saurin daukar makami suna fakewa a karkashin  addini ko jam’iyya ko kabila, inda suna barna inda suka yi kira gare su da su ji tsoron Allah su yi watsi da wannan mummunar dabi’ar.

A karshe sun yi kira ga gwamnatin Jihar Kaduna    kan ta zakulo tare da hukunta wadanda suka haddasa tashin hankalin tare da yin kira ga jama’ar Kudancin Kaduna su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu cikin lumana.