Gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewacin Najeriya da ake kira Coalition of Concerned Northern Forum, sun yi kira da Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa, NNPC Mele Kyari da wasu daraktoti da su gaggauta yin murabus kan gurbataccen man da aka shigo da shi cikin kasar daga ketare.
Makonni uku da suka gabata kasar ta fada cikin matsalar karancin mai, sakamakon gurbataccen man da aka shigo da shi, lamarin da ya janyo dogayen layuka a gidajen mai.
- Kar a biye wa PDP ko APC a Zaben 2023 —Kwankwaso
- NAFDAC ta kama ganda mai dauke da guba ta N23m a Legas
Kungiyar a wata sanarwa da ta fitar a wannan Lahadi mai dauke da sa hannun shugabanta da kuma kakakinta, Malam Ibrahim Bature da Kwamared Abdulsalam Moh’d Kazeem, sun yi Allah wadai da karancin man fetur da ake fama da shi a fadin kasar.
A kan haka ne suka bukaci a yi wa Hukumar Kula da Harkokin Man fetur ta Kasa (NNPC) garambawul karkashin jagorancin Mele Kyari, saboda abin da suka kira karya tarihin gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari na rashin ganin karancin mai tun hawansa mulki.
Mun dauki matakan kawo karshen karancin mai —NNPC
A makon da muka yi bankwana da shi ne Mele Kyari ya tabbatar da cewa, kamfanin NNPC ya samar da matakan shawo matsalar karancin man fetur da ake fama da ita yanzu a fadin kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kwamitin Majalisar Wakilai kan albarkatun man fetur a ranar Laraba ta makon jiya.
Kyari ya bayyana karancin man a matsayin wata matsala da ba a yi tunanin samun ta ba, amma ya ce jirage makare da man fetur na gab da zuwa Najeriya.
A cewarsa, janye jiragen mai guda biyar da aka yi dauke da man fetur din, shi ne ya haifar da karancin man, wanda hakan ya shafi zirga-zirgar ababen hawa.
Sai dai ya ce NNPC ya shigo da adadi mai yawan gaske daga kasar waje wanda zai cike gibin tare da dawo da daidaituwar al’amuran man fetur a kasar nan.
Kazalika, Kyari ya ce NNPC ya yi yarjejeniya tare da hadin gwiwa da masu shigo da man fetur don kawo ishasshen mai da zai kawo karshen matsalar man da ake fuskanta.
Tun da farko, shugaban kwamitin, Abdullahi Mahmoud, ya ce dole ne kamfanin NNPC ta tashi tsaye wajen gudanar da ayyukansa yadda ya dace.
Ya ce, abin da ya faru ya jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali, wanda ke iya ta’azzara abubuwa da dama saboda sakacin kamfanin.
Matsalar karancin man fetur ta yi muni musamman a Abuja, Legas da sauran wasu jihohin, har ta kai ga ana sayen litar mai a kan N600 a wasu jihohin.
Lamarin dai ya jefa dumbin mutane cikin mawuyacin hali na gaza yin zirga-zirga saboda tsadar ababen hawa yayin sufuri.