Masu rajin kare ’yancin dan Adam a karkashin kungiyar Democratic Socialist Mobement da ta Campaign for Democratic and Workers Right (CDWR) sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi maganin matsalolin da suka addabi bangaren wutar lantarki.
Barista Toluwani Adebiyi, wani lauya da ya samu nasara a kotu game da hana karin kudin wutar lantarki, ya fadi a wurin wani taro a Legas cewa akwai bukatar a samar da wata hanya ta dindindin da za ta yi aiki wajen magance matsalar bangaren wutar lantarki.
Ya fadi haka ne a taron na Lagas, inda ya nanata bukatar a samu hobbasa daga bangaren masu mulki da kungiyoyin mutane domin aiwatar da hukuncin na kotun.
Masu jawabai a wurin taron, sun soki matsayin kamfanonin rarraba wutar lantarki na cewa ba su samun riba, inda suka bayyana hakan da cewa karya ce kawai kuma wani yunkuri ne na cutar gwamnati da ’yan Najeriya, a daidai lokacin da suka mayar da kashi 80 na ma’aikatansu a matsayin ma’aikatan wucin-gadi lamarin da ya saba wa dokokin kwadago.
Sun ce tsare-tsaren gwamnatocin da suka gabata sun gaza ne saboda an gina su ne a kan tsari marar ’yanci irin na sayar da hannun jari.
A jawabin Kakakin kungiyar CDWR, Kwamared Chinedu Bosah, ya bukaci kungiyoyin unguwanni su rika taimakawa ta hanyar yin wasu ayyuka a unguwanninsu wanda hakan zai taimaka wurin samun tallafi.
A wani labarin, masu amfani da wutar lantarki a Unguwar Ijeshatedo, karamar Hukumar Surulere a Jihar Legas sun yi barazanar daina biyan kudin wuta na wata-wata ga Kamafanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko (EKEDC), matukar kamfanin bai saka musu mita mai kati a gidajensu ba.
Sun nuna bakin cikinsu ganin yadda suke biyan kudi mai yawa kan kiyasatawa alhali unguwanni masu makwabtaka da su suna biyan kudi kadan saboda suna da mitocin.
Wani mazaunin unguwar Ogunlana, Eniola Taiwo ya ce, masu amfani da wutar lantarki a yankin suna biyan kudin wutar da ya wuce misali inda suke biyan kudi daga Naira dubu 10 zuwa dubu 35 a kowane wata.
Taiwo, wanda shi ne Sakataren kungiyar Ci gaban yankin Ogunlana ya ce, “Duk da cewa mun yi kokari sosai wurin tabbatar da cewa kamfanin EKEDC ya samar mana da mitoci masu kati a yankin, abin ya ci tura domin har yanzu ba su rubuta mana martani ba kan takardar da muka rubuta musu.
“Mu mutanen Ijeshatedo muna nan a kan bakarmu na ganin an saka mana mitocin kafin mu ci gaba da biyan kudin wutar. Masu amfani da wutar lantarki a Lawanson da Mushin da Pako da Aguda da kuma Itire suna biyan kudi kadan saboda suna da mitocin, me ya sa aka ware Ogunlana?”
Wata ma’aikaciyar banki, Chinyere Akinfenwa, wacce take zaune a Unguwar Ogunlana ta ce ana kawo mata takardar kudin wuta ta Naira dubu 15 a kowane wata.
Wani mai dinki, Bode Aderasin wanda shi ma yake zaune a titin na Ogunlana ya bukaci kamfanin EKEDC, ya daina raba takardar biyan kudin wuta a yankin domin sun gaji da biyan kudin da ake kiyastawa.
“Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta kasa (NERC), ta ce dole ne duk kamfanonin rarraba wutar lantarki su samar da mitoci masu kati ga dukkan masu bukatar wutar lantarki don haka su ma kamfanin EKEDC ya kamata su bi ka’ida.”
Kehinde, wanda shi ma mazaunin yankin ne ya ce “Yaya za a ce kamfanin raba wutar lantarki ba za su bayar da mitoci ga abokan huldarsu ba. Wannan ba abin mamaki ba ne kawai, har ma da rashin sanin abin da ya kamata.” Da yake jawabi a kan barazanar, shugaban sashin hulda da jama’a na kamfanin, Ademola Adegoke ya ce kamfani na da tsarin saka wa duk abokan huldarsu mitocin a cikin shekara biyar.
Sai ya bukaci abokan huldar nasu wadanda suka bata wa rai su kara hakuri, kuma ya ce yana tabbatar musu mahukuntan kamfanin za zu duba kokensu.
Adegoke ya ce amma mutane su biya kudin wutar da suka yi amfani da ita, kuma ya bukaci wadanda ba za su iya jira har lokacin da kamfanin zai kawo musu mitar ba, su nema ta hanyar tsarin CAPMI.
kungiyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta magance matsalar wutar lantarki
Masu rajin kare ’yancin dan Adam a karkashin kungiyar Democratic Socialist Mobement da ta Campaign for Democratic and Workers Right (CDWR) sun yi kira ga…