Wasu kungiyoyi 150 a Jihar Borno sun hada kai don saya wa Gwamna Babagana Umara Zulum fom din sake tsayawa takara kan Naira miliyan 50.
A cewar wani rahoto, kungiyoyin sun nemi Gwamna Zulum ya sake tsayawa takara a karkashin jam’iyyar APC ranar Juma’a a Maiduguri, baban birnin jihar.
- Dan kwangila ya ki kawo wa APC fom din takarar 2023
- ‘Ya kamata a binciki duk wanda ya sayi fom din takarar APC N100m’
Kakakin kungiyoyin, Umar Shettima, ya ce sun bukaci Zulum ne da ya ci gaba da rike mukaminsa bisa la’akari da ayyukan da ya yi a dukkanin bangarori a wa’adinsa na farko bisa jagorancin jihar.
Shettima wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Kasa Reshen Jihar Borno, ya ce “Kungiyoyi masu rajista ne suka hada gwiwa tare da kwararrun malamai, bangaren kiwon lafiya, tallace-tallace, sufuri da kungiyoyin mata da sauran su don aiwatar da wannan kuduri.
“Muna da kudurin tabbatar da cewa Farfesa Babagana Umara Zulum ya ci gaba da zama a ofis, bayan da ya kawo irin nasarorin da ba a taba gani ba a duk fannonin rayuwa cikin shekara uku kacal a kan mulkin Jihar Borno.
“Muna kira gare shi da ya sake tsayawa takara karo na biyu domin ya ci gaba da ayyukan alheri da yake yi wa mutanen Borno.
“Kungiyoyin sun yanke shawarar siyan fom din ne don nuna sha’awa da neman tsayawa takarar Gwamna Zulum a zaben 2023,” inji Shettima.
Ya kuma bukaci al’ummar Borno su ma su bayar da goyon bayansu ta hanyar bayar da gudumawa a wani asusu na musamman, wanda za a bayyana bayanansa daga baya domin ana bukatar kudi don yakin neman zaben da ke tafe.