✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar ’yan sintiri za ta taimaka a gudanar da zaben 2015

Mataimakin kwamandan kungiyar ’yan sintiri ta Najeriya na jihohin Arewa ta Tsakiya Alhaji Garba Juji ya bayyana cewa kungiyarsu ta shirya don taimaka wa gwamnati…

Mataimakin kwamandan kungiyar ’yan sintiri ta Najeriya na jihohin Arewa ta Tsakiya Alhaji Garba Juji ya bayyana cewa kungiyarsu ta shirya don taimaka wa gwamnati da sauran al’ummar Najeriya don a gudanar da zabubbukan shekarar 2015 lafiya. 

Alhaji Garba ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos a makon jiya.
Ya ce babu shakka idan aka sanya ’yan sintiri a cikin gudanar da zabubbukan masu zuwa, to za a yi lafiya a tashi lafiya.
“Mu ’yan sintiri kanmu a hade yake, muna cikin al’umma ne babu ruwanmu da maganar kabilancin ko kuma addini. A cikinmu akwai kowace irin kabila da ke kasar nan, kuma akwai mabiya kowane addini a kasar nan.” Inji shi.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su sanya ’yan sintiri a cikin jami’an tsaron da za su lura da harkokin zaben da za a gudanar, “yin hakan zai sa mu bada gudunmuwar don tabbatar da zabe mai inganci.”
“Ina kira ga dukkan ’yan kungiyar sintiri ta Najeriya su rike wannan aiki bisa amana da kishin kasa.” Ya ce daga karshe.