Hadaddiyar kungiyar ’Yan Kasuwar Neja ta zabi shugabanninta a karashin shugabancin Alhaji Muhammad Abubakar dandare, bayan da abokin takararsa, Alhaji Barde Bawa ya janye jim kadan kafin zaben da aka gudanar a zauren taron Cibiyar Marigayiya Maryam Babangida a Minna.
Malam Ahmad Idris shi ne Mataimakin Shugaba na 1 da Alhaji Shehu Attahiru, Mataimakin Shugaba na 2. Alhaji Muhammad Garba Garkuwa ne ya zama Sakatare, sai Malam Ibrahim Yellow, Jami’in Hulda da Jama’a. Malam Abdul-Mumuni dangwari ne Shugaban Matasa, sai Liyatu Ishaku, Shugabar Mata da Florence Anthony, Mataimakiyarta.
Sabon Shugaban, Alhaji Muhammad ya yi bukaci gwamnatoci, a dukkan matakai, su rika ware wa fannin kasuwanci wani kaso na musamman, wanda zai taimaka wajen farfado fannin, ta yadda za a samu gogayya da sauran kasashen da suka cigaba.
Ya jaddada cewar ’yan kasuwa na taka muhimmiyar rawar samar da hajoji a wuraren da ake bukata, don haka ya kamata gwamnatoci su rika bayar da gudunmawa don samar da hajoji cikin farashi mai rahusa.
Ya yi kira ga ’yan kasuwa su cigaba da nuna halayen kwarai ga duk wadanda suke hulda da su. “Duk dan kasuwa da yake kamanta gaskiya a harkokinsa, ya fi samun abokan hulda da kuma bunkasar harkokinsa cikin lokaci kankane, sannan zai samu babban rabo daga Allah, kuma Ya albarkaci dukiyarsa”. Inji shi.
Malam Labaran Sarkin Kaji, daya daga cikin wadanda suka gudanar da zaben, ya nuna gamsuwa da farin cikin yadda ’yan takara da magoya bayansu suka nuna halin ya-kamata a yayin zaben har aka kammala shi.
Ya ce kwamitinsu ya yi dari-dari game da lamarin zaben, amma daga baya da ya jajirje, cikin taimakon Allah, sai ga shi ’yan kasuwan suka tabbatar da matsayinsa a na ’yan uwantaka, domin buri kowanensu sai ya kasance don ciyar da kungiyar gaba ne.
kungiyar ’Yan Kasuwar Neja ta zabi shugabanninta
Hadaddiyar kungiyar ’Yan Kasuwar Neja ta zabi shugabanninta a karashin shugabancin Alhaji Muhammad Abubakar dandare, bayan da abokin takararsa, Alhaji Barde Bawa ya janye jim…