Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Gwari ta Jihar Bauchi, Alhaji Sani Abubakar ya bayyana irin gudummowar da suke bayarwa wajen horas da matasa yadda za su koyi sana’ar sayar da kayan marmari domin ganin sun dogara da kansu.
Shugaban ya bayyana haka ne cikin hirarsa da wakilinmu a ofishinsa da ke kasuwar Muda Lawal a Bauchi, inda ya ce kungiyar tana horas da matasa yadda za su kasance masu hakuri ta hanyar saye da sayarwa da dakon kaya da saukewa da sauran hanyoyin da mutane za su amfana.
Ya ce a duk loakacin da mutum ya yi sammako ya zo kasuwar, iske ana gudanar da hada-hadar kasuwanci, kuma suna da masu sa ido don ganin ba a cutar da mai saye ko sayarwa ba. Kuma idan sun samu bata-gari sukan fitar da shi daga kasuwar.
Game da kayan da suke sayarwa, ya ce sukan sayar da kayan lambun da ake nomawa a Jihar Bauchi ne, amma daga watan shida sukan fita wasu jihohi don nemo kayan da ake bukata.
Shugaban ya yaba wa gwamnatin Jihar Bauchi game da yadda ta fadada kasuwar, ta sanya kwalta tare da yin gini irin na zamani, ta samar da lantarki da ruwan famfo da ake amfani da shi don tsabtace kayan da ake sayarwa don inganta harkokin masu sana’ar gwari.
Daga karshe ya yi kira ga jama’arsa su kasance masu hakuri da kamanta gaskiya a sayensu da sayarwarsu. Idan mutum yana da gaskiya ko ya karye, Allah zai tallafa Ya farfado da shi. Sannan ya roki gwamnati ta rika tallafa wa masu wannan sana’a, kamar yadda ake tallafa wa sauran masu sana’o’i da makamantansu don su samu ci gaba fiye da halin da suke a yanzu.
kungiyar ’yan kasuwar gwari a Bauchi na taimakon matasa kan sana’ar kayan lambu
Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Gwari ta Jihar Bauchi, Alhaji Sani Abubakar ya bayyana irin gudummowar da suke bayarwa wajen horas da matasa yadda za su…