A makon jiya ne Kungiyar ’Yan fansho ta Ma’aikatan Tarayya ta gudanar da zaben shugabanninta da za su ja ragamar shugabancinta na tsawon shekara hudu.
An zabi Malam Isyaku Umar a matsayin Shugaba sai kuma Malam Haruna Usman a matsayin Mataimakin Shugaba.
Sauran sun hada da Sanusi Lawan a matsayin Ma’aji, sai kuma Jamilu Ado a matsayin Odita. Haka an zabi Abdulwahab Lawan da Abdul Lawan Danlami a matsayin Amintattun Kungiya.
A lokacin da yake jawabi yayin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar, Shugaban Kwamitin Zaben Mista A. A. Williams ya bayyana cewa ya gamsu da yadda zaben ya gudana, lura da yadda masu zaben suka gudanar da zaben cikin hadin kai da farin ciki.
Shi ma a nasa jawabin sabon Shugaban Malam Isyaku Umar ya gode wa ’yan uwansa ’yan fansho da suka zabe shi, kuma ya yi alkawarin tafiya da kowa wajen gudanar da ayyukan kungiyar.
A cewar sabon shugaban zai yi duk abin da ya dace wajen ganin an kwato wa ’yan uwansa ’yan fansho hakkokinsu, ksancewar yawancin ’yan fansho suna fuskantar matsaloli na rahin biyansu garatuti da kudin fanshonsu na wata-wata.