✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar ’yan banga a yankin Jankwe ta zabi shugabanni

An rantsar da shugabannin kungiyar ’yan banga na yankin rayawa na Jankwe da ke karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa. Bikin, wanda aka gudanar a…

An rantsar da shugabannin kungiyar ’yan banga na yankin rayawa na Jankwe da ke karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa.
Bikin, wanda aka gudanar a sakatariyar yankin rayawar da ke garin Agyaragu, ya sami halartar jama’a da dama.
Wadanda aka rantsar a matsayin sababbin shugabannin kungiyar, sun hada da Mista Atala Bulus, a matsayin shugaba da Muhammed Musa Ibrahim mataimakinsa; Muhammed Musa Hantsu ya zama sakatare da Muhammed Adamu mataimakinsa. Luka Jatau shi ne ma’aji, sai Safiyanu Sa’idu sakataren kudi. Shagari Makwe shi ne mai horo; Ibrahim Madaki Odita; Sunday Stephen Ayuba, jami’in hulda da jama’a (PRO), Yakubu Fata Sama’ila, jami’in hulda da jama’a na 2 (PRO2), Ishaku Yagu,mai kula da fannin ’yan fashi da makami. Ibrahim Akwayi, shi ne Sajen kungiya da Friday Akudu Saje na 2, sai kuma Sa’idu Adamu a matsayin Kofur, alhalin Samuel Akwe ne mai tabbatar da tsaro, da Okeh Sunday Gana, jami’in kula da sha’anin tsaro, sai Augustine Iyele Iliya, jami’i mai kula da sintiri.
A jawabinsa, Jami’in Gunduma na ’yan sanda (DPO) mai kula da yankin Idris Muhamed ya jinjina wa kungiyar kan gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Ya yi nunin kyakkyawar dangantakar tsakanin ’yan sanda da ’yan banga a yankin, saboda haka ya bukaci sababbin shugabannin su tabbatar da dorewar hakan. Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni a yankin da ma jihar baki daya da su rika taimaka wa ’yan banga, musamman da kudi don inganta ayyukansu na dakile ayyukan batagari.
DPO Idris ya bukaci ’ya’yan kungiyar su ba sababbin shugabannin cikakken hadin kai don cimma nasara. Ya nemi al’ummar yankin, musamman matasa su kaurace wa karya doka, saboda guje wa hukuncin ba sani ba sabo.
Shi ma a jawabinsa, sabon zababben shugaba, Mista Atala, a madadin wadanda aka rantsar, ya jinjina wa tsohon shugaba dangane da gudummawar da ya bayar har kungiyar ta kai ga samun gagarumar nasara a lokacinsa. Ya gode wa ’yan kungiya kan zaben kuma ya bukaci hadin kansu don bunkasa kungiyar har a kai ga cimma burin kafa ta.