kungiyar ’yan asalin Arewacin Najeriya mazauna Amurka mai suna Arewa Progressibe Forum (APF-USA) tana yi wa daukacin al’ummar Musulmi musamman wadanda suke zaune a Arewacin Najeriya murnar Barka da Sallah.
kungiyar ta aiko da wannan sako ne ne ta ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja a ranar Talatar da ta gabata.
Takardar dauke da sanya hannun Shugabanta Umar Muhammed da kuma Sakatarenta Martins Ocholi, ta taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar Sallar Layya.
kungiyar ta kuma yi tsokaci a kan ziyarar da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mista John Kerry ya kai Najeriya a kwanakin baya bayan Sakataren ya nanata kudurin Amurka wajen yin daidaito a tsakanin maza da mata wajen neman ilimi a kowane bangare na Najeriya.
kungiyar ta ce wannan batu na Mista John Kerry ya yi mata dadi idan aka yi la’akari da yadda aka yi wa bangaren Arewacin Najeriya nisa ta fuskar neman ilimin zamani musamman ga matan da ke yankin. “kungiyar ’yan Arewa mazauna Amurka tana taya daukacin al’ummar Musulmi musamman wadanda ke Arewacin Najeriya murnar zagayowar Sallar Layya. Muna fatan al’ummar Musulmin duniya musamman na Arewacin Najeriya za su gudanar da bikin Sallar Layya cikin lumana ba tare da samun matsala ba”, inji sanarwar.
kungiyar ’yan Arewa mazauna Amurka, kungiya ce mai zaman kanta da aka kafa don ci gaban Arewacin Najeriya ta fuskar ganin an samu daidaito a tsakanin maza da mata a bangaren neman ilimi. kungiyar takan tallafa wa yankin Arewa ne ta hanyar daukar nauyin mata musamman mazauna karkara da ba su da karfin zuwa makaranta domin su samu ilimi. Haka kuma kungiyar kan tallafa wajen gyara makarantun da ke yankin Arewa musamman wadanda suke karkara kuma suka lalace don ganin an samu bunkasar ilimi.
Sannan kungiyar takan ba mata tallafin karo ilimi (scholarship) tun daga matakin firamare zuwa sakandare zuwa Jami’a musamman ga ’ya’yan talakawa masu kwazo da iyayensu ba su da halin daukar dawainiyar karatunsu amma ga wadanda ke zaune a Arewacin Najeriya.
kungiyar ta ce tuni ta fara kokarin hada kai da jihohin Arewa ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja don ganin ta cimma burin bunkasa ilimi a yankin.
kungiyar ’yan Arewa mazauna Amurka ta gamsu da ziyarar John Kerry Najeriya
kungiyar ’yan asalin Arewacin Najeriya mazauna Amurka mai suna Arewa Progressibe Forum (APF-USA) tana yi wa daukacin al’ummar Musulmi musamman wadanda suke zaune a Arewacin…