Kungiyar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubkar, mai suna Atiku Arewa Reporters ta janye goyon bayanta gare shi a Kano.
Shugaban kungiyar, Abdallah A. Gama, ya ce akalla mutane miliyan biyu ne da suka hada da shugabanni da mambobi daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya da Abuja suka ajiye tafiyar Atiku, saboda zargin rashin kyautawa da kuma watsi da su.
- Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 19 a Gamboru Ngala
- Shugaban Chadi ya nada tsohon abokin adawar mahaifinsa Fira Minista
- DAGA LARABA: “Mun Ci Karfin Aikin Zaben 2023” – Shugaban INEC
Baya ga haka, ya yi zargin ana nuna musu halin ko-in-kula a jamiyyar PDP da ma harkar Atikun, shi ya sa “Daga yau, wannan kungiya ta mu ta ajiye tafiyar Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP.
“Siyasa ba za ta yiwu kamar bauta ba, duk abin da za ka yi sai a ce sharadin sai an dare karagar mulki sannan a biya ka da mukami.
“Idan za a tafi wurinsa (Atiku), muna zuba manmu a mota, mu kama otal, sannan mu sallami daukacin mutanen da suka je wurin.
“Amma sai aka ce sai an ci mulkin za a saka mana. Idan kuma ba a ci mulkin ba fa?”
Gama, ya kara da cewa za su ci gaba da tuntuba domin neman makomar kungiyar nan ba da jimawa ba.