✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar wayar da kai ta ilmantar da jama’ a kan zaben shugabanni nagari

Wata kungiya mai zaman kanta, mai rajin kafa nagartacciyar gwamnati, ta ilmantar da jama’ar garin Dawakin Tofa a Jihar Kano a game da yanda za…

Wata kungiya mai zaman kanta, mai rajin kafa nagartacciyar gwamnati, ta ilmantar da jama’ar garin Dawakin Tofa a Jihar Kano a game da yanda za su gabatar da bukatunsu ga shugabannin siyasa, a maimakon su aiwatar musu da aikin da ransu ya raya musu.
A yayin da yake jawabi a taron tattaunawa na al’umma a yankin na Dawakin Tofa, Jami’ in kungiyar, Malam Abba Isyaku ya bayyana cewa suna aikin gwaji ne a kananan hukumomi 3 a jihohin Kano da Kaduna da kuma Jigawa.
Ya ce sun bullo da wannan shirin ne domin samar ga ingantacciyar gwamnati, wacce za ta samar da ababen more rayuwa masu inganci ga jama’a tare da tabbatar da gaskiya da amana ta jami’an gwamnati a matakin kananan hukumomi.
Ya ce, “Wannan tsari ne da ya baiwa talakawa damar su bayyana wa masu neman zama shugabannin gwamnati bukatunsu da abubuwan da suka dame su, sabanin tsarin baya inda masu neman mukamai suke bayyana alkawuransu tare da aiwatar da ayyuka a kan wadannan alkawuran da suka dauka.”
Ya ce makasudin abin ba na samar da ababen more rayuwa ga jama’a ba ne kadai, ya hada har ma da sa ido da bin diddigin yanda ake aiwatar da ayyukan tare da gani cewa komai yana tafiya daidai wajen gudanar da wadannan ababen more rayuwa.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar cigaban jama’ar Dawakin Tofa, Malam Zahraddeen Aminu ya ce sun dauki bakuncin taron ne domin su samar wa kansu mafita game da shugabancin karamar hukumarsu.
Ya ce sun kafa kungiyyar ne domin maganta matsalolin al’umar yankinsu, sannan kuma kungiyar tana da rassa a dukkanin mazabun yankin, lamarin da zai ba su dama su isar da wannan sako na wayar da kai ga jama’a na dukkanin mazabun yankin.
Haka shi ma a nasa jawabin, shugaban makarantar Sakandare ta Gwamai a yankin, Malam Aminu Sanusi Idris, ya bukaci jama’a su hada kansu tare da tsoma baki a cikin harkokin mulkin karamar hukumarsu tare da sa ido a kan yanda ake aiwatar musu da aikace-aikace, musamman na harkar ilimi da lafiya da ruwan sha da sauransu, tare da tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai.