Kungiyar Watford ta Ingila ta dauki golan Najeriya, Maduka Okoye daga kungiyar Sparta Rotterdam ta Holland.
Okoye ya amince da yarjejeniyar shekara biyar da kungiyar, sai dai ba zai fara tsaron ragar Watford din ba sai a Janairun badi.
- Kalubalen da ke gaban sabon kocin Barcelona Xavi
- Kungiyoyin agaji sun horar da ’yan sa-kai 50 a Gombe
Kungiyar ce ta sanar da hakan, inda ta ce, “Kungiyar Watford FC na farin cikin sanar da cewa ta kulla yarjejeniya da gola mai tashe a yanzu, Maduka Okoye na shekara biyar daga Janairun 2022.”
Okoye ne golan farko a kungiyar Sparta Rotterdam na Holland, inda shi ne ya kama dukan wasannin da kungiyar ta buga a kakar bana.
Kafin Spart Rotterdam, ya kama gola a kungiyar Fortuna Dusseldorf II ta Jamus, da Jong Sparta da Holland.
A kakar bara ma, golan ya buga wasa ba a zura kwallo a ragarsa.
Yanzu haka shi ne gola zabin farko a tawagar Super Eagles, kuma shi ake sa ran zai kama wasan Najeriya da Laberiya a ranar Asabar mai zuwa.
An haifi Okoyo a Jamus kuma mahaifinsa dan Najeriya ne, mahaifiyarsa kuma ’yar Jamus.