✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Waiwaye ta karrama Aminiya

A ranar Asabar da gabata, kungiyar Waiwaye Adon Tafiya a Jihar Kano ta bayar da shaidar girmamawa ga Jaridar Aminiya.A lokacin da yake bayar da…

A ranar Asabar da gabata, kungiyar Waiwaye Adon Tafiya a Jihar Kano ta bayar da shaidar girmamawa ga Jaridar Aminiya.
A lokacin da yake bayar da shaidar karramawar, shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Mandawari ya bayyan cewa kungiyar ta kuduri aniyar bayar da wannan shaida ce ga jaridar bisa ga irin taimakon da take bayarwa wajen bunkasa harshen Hausa.
kungiyar, wacce ta samo asali daga wani shiri da ake gabatarwa a gidan Rediyon Freedom, ta bayar da wanann shaida ce a lokacin da take gudanar da Bikin Makon Hausa, wanda ta shirya don bunkasa harshen tare da farfado da al’adun Hausawa.
Taron, wanda shi ne irinsa na farko a tarihin kungiyar, an dauki kwana biyar ana gudanar da shi, inda manyan malaman jami’a suka gabatar da makaloli daban-daban a kan adabi da kuma al’adun Bahushe da sauran bangarori. Har ila yau, a wajen wannan biki an gabatar da wasannin da suka hada da wakokin Hausa da nazari a kan wakokin gargajiya da sauransu.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Muhammad Mandawari ya bayyana cewa kungiyar ta dauki nauyin gudanar da wannan shiri na Makon Hausa ne da nufin a tattaunawa game da rayuwar Bahaushe gaba daya, dangane da abin da ya shafi al’adunsa da dabiunsa da tsarin zamantakewarsa. “Muna burin mu ga cewar Bahaushe ya farka, ya farfado da ainihin al’adunsa, musamman masu kyawun ciki, ya kuma yi kokarin wajen ganin ya dawo da abubuwan da suka saraya na abin alfaharinsa.
Ya bayyana cewa sun hada kai da jami’a wajen gudanar da wannan taro ne, “ganin irin manufarmu ya sa malaman jami’a wadanda dama su aka sani da koyar da wannan harshe a jami’a suka ba mu goyon baya dari-bisa-dari. Kamar yadda aka sani malamn jami’a kokarin da suke yi shi ne su suke koyarwa su kuma wadanda aka koyarwar suke dawowa cikin al’umma, su aiwatar da abin da suka koyo a jami’a. Don haka idan an duba wannan abin da muke yi, wani dori ne a kan abin da malaman ke yi a jami’a shekara da shekaru.
A cewar Ibrahim Mandawari, kungiyarsu tana kokarin janyo matasa su fahimci al’adun Hausawa, musamman ganin cewa a kullum gari ya waye, al’adun Hausawa suna saraya tare da bacewa. A cewarsa, fahimtar hakan ne zai sa matasan su san martabar harshen tare da yin kishinsa.  “Mun lura cewa al’adun Hausawa a kullum saraya suke, don haka muka dauki damarar janyo matasa su fara fahimtar al’adun Hausawan. Sannan daga bisani mu nuna musu muhimmanci kishin harshen da sauransu. Wani abin
sha’awa, kashi 80 na mutanen da ke cikin dandalin nan matasa ne wadanda kishin harshen ya sa suka zabi zama a wananna kungiya a maimakon su kai kansu wasu dandalin na kafar sadarwa ta zamani ta WhatsApp wadanda suka shafi nishadi da sauransu.”
A jawabinsa, shugaban taron Farfesa dandatti Abdulkadir, wanda ya sami wakilcin Dokta Yakubu Magaji Azare, ya bayyana muhimmancin da harshen Hausa ke da shi duba da yadda a yanzu Turawan yamma suka dukufa wajen yin nazarin harshen a matakin jami’a, inda aka samu manyan farfesoshi daga cikinsu suna nazartar harshen. “Saboda sanin muhimmancin da harshen Hausa ke da shi da kuma yawan masu magana da shi a duniya ya sa ya zamo daya daga cikin manyan harsunan da kafafen watsa labarai ke yin amfani da su wajen watsa shirye-shiryensu da manufofinsu. Irin wadannan kafafen watsa labari sun hada da BBC da Muryar Amurka da Jamus da Faransa da China da Egypt da sauransu. Hakan ya sa a yanzu an samu Turawan yamma da suke nazartar harshen a matakin jami’a, inda har aka samu farfesoshi daga cikinsu” Inji shi.
Farfesan ya jinjina wa kungiyar ta Waiwaye game da wannan taro da suka shirya, inda ya bayyana cewa “A tarihi ba a taba samun wata kungiya ta shirya irin wannan taro na Makon Huasa sukutum da guda ba. Wanann yana nuni da irin yadda wannan kungiya ta dauki harshen Hausa da matukar muhimamnci tare da kuma kishinsa.