Rahotannin da ke fitowa sun nuna kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) ta tafi gasar cin kofin matasa na Afirka ne da ke gudana a Senegal ba tare da an biya ’yan kwallon da masu horar da su alawus-alawus dinsu ba.
Wata majiya da ta fito daga Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce saboda karancin kudin da hukumar ke fuskanta ne ta sa aka kasa biyan ’yan kwallon da jami’ansu alawus-alawus dinsu kafin su tafi gasar.
Sai dai majiyar ta tabbatar yanzu haka hukumar tana yin duk mai yiwuwa don ganin ta biya ’yan kwallon da jami’an nasu.  Haka kuma majiyar ta ce hatta ’yan kwallon Golden Eaglets (U-17) da suka lashe gasar cin kofin duniya na matasa da ya gudana a Chile har yanzu ba a biya su hakkokinsu ba sabili da rashin kudi.
Wata majiya ta ce akwai alamun za a biya ’yan kwallon U-23 basussukan da suke bi kafin a kammala gasar da ke gudana a Senegal.
Idan za a tuna kocin kungiyar U-23 Samson Siasia ya koka kafin a fara gasar cin kofin matasa na Afirka a Senegal saboda rikon sakainar kashin da Hukumar NFF ta yi musu.
Ya ce kada wani ya zarge shi idan Najeriya ta kasa kai bantenta a gasar saboda rashin biyansu albashi da wasu daga cikin hakkokinsu a kan lokaci.
…kungiyar U-23 ta tafi gasar ce ba tare da kudi ba
Rahotannin da ke fitowa sun nuna kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) ta tafi gasar cin kofin matasa na Afirka ne…