✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Tsofaffin daliban UDU za ta taimaka wa matasa

Mataimakin Shugabar kungiyar Tsofaffin daliban Jami’ar Usmanu danfodiyo (Usman Danfodio Unibersity -UDU) da ke Sakkwato, Malam Sa’id Suleiman Farin Wata, ya jaddada kudurinsu na  kara…

Mataimakin Shugabar kungiyar Tsofaffin daliban Jami’ar Usmanu danfodiyo (Usman Danfodio Unibersity -UDU) da ke Sakkwato, Malam Sa’id Suleiman Farin Wata, ya jaddada kudurinsu na  kara bullo da shirye-shiryen da za su taimaka wa  matasa su zama masu dogaro da kansu ta kowace fuska, musamman horar da su sana’o’i.
Malam Sa’id Suleiman ya bayyana  haka ne yayin da ya ke zantawa da Aminiya a Minna, inda ya ce yin haka yana daya daga cikin matakan da za su bi wurin gina kasa ta kai ga matsayin da ake tsammani na shiga jerin kasashen da suka ci gaba .
Mataimakin Shugaban ya jinjina wa ’ya’yan kungiyar, musamman wadanda suka assasa harsashinta har ta kai matsayinta a yau tare da rassa a jihohin Arewa da kuma Kudu, don haka za su yi tsaye wurin kara yawan rassan  a sauran jihohin da babu su a halin yanzu domin fadada aiwatar da ayyukanta.
Daga cikin nasarorin kungiyar, Malam Sa’id ya ce akwai tsayuwarta da kafafunta; hadin kan ’ya’yanta da shugabanninta da ma iyayenta da suka hada da wasu sarakuna da suka bayar da gudunmuwa a fannoni daban-daban.
Ya ce wasu nasarorin sun hada da tuntunbar juna akai-akai; da samun ziyartar jami’ar tare da tattauna matsalolin da suke addabarta da nemo hanyoyin da za su taimaka wurin shawo kan wasu daga cikinsu, bisa la’akari da cewar jami’ar tana fama da dimbin matsaloli.