Makarantun koyon ayyukan unguwar zomo da harkokin kula da lafiya da ke Ningi da ta cikin garin Bauchi, sun samu tallafi daga kungiyar kula da lafiya ta duniya, wato Tship da ke karkashin kulawar Hukumar Tallafa wa Ayyukan Raya kasa ta Amurka (USAID). Tallafin an bayar da shi ne don kula da harkokin lafiyar al’umma wadanda suka hada da rage mace-macen mata masu juna biyu a Jihar Bauchi
Shugaban kungiyar Tship, Dokta Habib Sadauki, shi ne ya mika kayayyakin ga shugabannin makarantun da kuma jami’an ma’aikatar lafiya ta Jihar Bauchi, domin ganin an inganta tsarin koyar da dalibai ta hanyar wadata su da kayan aikin da suka dace a lokacin da suke makaranta saboda a samu ingantaccen ilmi da kwarewa a fagen kiwon lafiya.
An shirya taron bita a Otel din Zaranda da ke Bauchi, a Litinin din da ta gabata, inda aka gabatar da jawabai game da matsalolin da ake fuskanta a irin wadannan makarantu, musamman na rashin kayan aiki da suka hada da gwaji da sinadaran aiki da takardun da suka dace. Don haka kungiyar ta samar da kayan saboda kowane dalibi ya samu kwarewar da ta dace a fannin kiwon lafiyar jama’a.
Dokta Habib Sadauki, ya ce suna son ganin mata suna zuwa asibiti awo tare da karbar magani da kuma kai yara wajen karbar allurar rigakafi, amma hakan ba zai samu ba sai da wadatar kwararrun ma’aikata da suka samu horon da ya dace ta yadda za su rika ilmantar da iyaye mata yadda za su rika bayar da agajin farko a duk lokacin da rashin lafiya ta samu yaran su, ko kuma lokacin da aihuwa ta tashi a gida ba a samu zarafin zuwa asibiti a kan lokaci ba.
Cikin kayayyakin da suka bayar akwai na’urori da littafan binciki da talabijin irin na zamani wadanda za a yi amfani da su wajen ganin an samu ilmi cikin sauki da sahihiyar fahimta, kuma an fara wannan aiki a jihar Bauchi lamarin da ya samar da ci gaba a fagen kiwon lafiya saboda tallafin da gwamnatin Bauchi da manyan jami’an sashen kiwon lafiya suke bayarwa wajen inganta harkokin kiwon lafiya. Don haka ya nemi iyaye da mazaje su rika nuna sanin ya kamata wajen inganta lafiyar su ta hanyar zuwa asibiti a kan lokaci.
Dokta Mohammed Sambo Liman shugaban hukumar lura da asibitoci ta Jihar Bauchi shine ya wakilci kwamishinan lafiya na Jiha Dokta Sani Abubakar Malami ya godewa kungiyar game da wannan tallafi, na Tship, kuma ya bayyana cewa za su yi tsaiwar daka wajen ganin an horas da daliban yadda ya dace tare kuma da sanya ido ga ma’aikatan don yin abin da ya dace wajen ganin anyi amfani da kayan yadda ya dace.
kungiyar Tship ta tallafa wa makarantun koyon aikin lafiya a Jihar Bauchi
Makarantun koyon ayyukan unguwar zomo da harkokin kula da lafiya da ke Ningi da ta cikin garin Bauchi, sun samu tallafi daga kungiyar kula da…