Shugabar kungiyar da ke rajin kare martabar malamai da inganta ilimi mai lakabin Theocy Charity Foundation, Misis A.Y Theodora, ta ce kungiyar ta kammala shirye-shirye don zagaya daukacin jihohin kasar nan da zimmar karfafa wa malamai gwiwa a kan aikinsu na malanta.
Theodora ta yi furucin ne yayin da take tattaunawa da Aminiya a Abuja a karshen makon jiya.
Ta ce “Mun kammala shirye-shirye don zagayawa jihohin kasar nan don mu wayar da kan malamai mu fadakar da su cewa aikin malantar da suke yi aiki ne mai mutunci da matsayi”.
Ta bayyana cewa kamata ya yi malamai su rike mutuncinsu kuma su sani cewa aikin malanta ba abin rainawa ba ne.
Ta ce amma abin takaicin shi ne malamai da yawa sun jahilci hakan saboda haka sai halayen da suke nunawa ya janyo ake raina aikin da suke yi.
Daga nan ta ce ba komai ne ya janyo wasu ke raina aikin malanta ba sai irin yadda gwamnati ba ta mayar da aikin malanta ba komai ba.
A fahimtarta wajibi ne sai gwamnati ta daraja tare da girmama malamai sannan mutane za su sauya irin kallon da suke yi wa malamai da aikin malanta a kasar nan.
Thoedora ta ce ta fi son a rika yi mata lakabi da “Malama” kafin a fadi sunanta kamar yadda ake yi wa lauyoyi da makamantansu saboda kimanta aikinta na malanta.
“Ba abin kunya ba ne idan mu ma malamai ana kiranmu da sana’armu kamar yadda ake yi wa likitoci da lauyoyi da kuma injiniyoyi,” inji ta.
To amma a cewarta a maimakon haka wasu malamai da yawa suna jin kunya a rika kiransu malamai ko a rika alakanta su da aikinsu.
Ta kara da cewa malamai abin koyi ne ga dalibai da al’umma don a ganinta malami ya fi kowa muhimmanci a rayuwa saboda irin gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta dan Adam.
kungiyar TCF za ta karfafa wa malamai gwiwa
Shugabar kungiyar da ke rajin kare martabar malamai da inganta ilimi mai lakabin Theocy Charity Foundation, Misis A.Y Theodora, ta ce kungiyar ta kammala shirye-shirye…