Wata kungiyar fafutikar samar da shugabanci nagari tare da wayar da kan masu zabe mai suna ‘Katsina Leadership Forum’ ta shirya muhawarar zantawa da ’yan takarar gwamna a jihar a karkashin jam’iyyu daban-daban don yin bayani a kan manufofinsu.
Shugaban kungiyar Injiniya Abu Amin ya bayyana hakan a Abuja a makon jiya, inda ya ce shirin wanda za a rika gudanarwa a Abuja, zai ba jama’a damar yi wa ’yan takara tambayoyi ta hanyar amfani da kafofin sadarwa na social media.
daya daga cikin ’yan takarar gwamna a jihar a jam’iyyar PDP, Ahmad Amin ’Yar’aduwa shi ne dan takara na farko da ya halarci shirin, ya bayyana cewa, idan ya samu nasarar zama gwamnan Jihar Katsina, zai kafa tsari da zai kula da nakasassu da mata da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a matsayin muhimman abubuwa da zai sa a gaba.
’Yar’aduwa wanda tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina ne, ya koka a kan yadda ilimin boko ya samu koma baya a jihar.
Ya ce Allah ya albarkaci Jihar Katsina da jami’o’i har guda 3, amma an gaza cin moriyarsu yadda ya kamata a sakamakon rashin ingancin karatu a makarantun firamare da sakandare na jihar.
Ya ce gwamnatinsa za ta inganta ilimin malaman makarantun ne ta hanyar daukar nauyin karatunsu, don su samu shaida mafi karanci da ake bukata a karantarwa a makarantun firamare da sakandare.
A jawabin rufe taron, sakataren kungiyar, Malam Sanusi Tasi’u Saulawa ya ce kungiyar Katsina Leadership Forum ba ta da niyyar goyon bayan kowane dan takara, sai dai za ta gayyace su daya bayan daya don yi wa al’ummar jihar manufofinsu.
kungiyar shugabanci nagari a Katsina ta gayyaci ’yan takara kan manufofinsu
Wata kungiyar fafutikar samar da shugabanci nagari tare da wayar da kan masu zabe mai suna ‘Katsina Leadership Forum’ ta shirya muhawarar zantawa da ’yan…