Shugaban kungiyar raya unguwar Sha’iskawa da kewaye da ke cikin garin Katsina, Mafawakin Majidadi, Alhaji Sani BK ya ce kungiyar ta mike wajen tallafa wa matasan yankin. Tallafin kuwa shi ne na fannin sama musu takardun karo ilmi a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa da kwalejojin Kimiya da Fasaha da ta Tarayya da ke cikin jihar da ma sauran makarantu a kasa baki daya.
Alhaji Sani ya shaida wa Aminiya haka ne kuwa a wata ganawa da ya yi da ita, inda ya kara da cewa, kungiyar na tallafa wa sauran daliban da kan samu matsala a jarabawarsu don su gyara ko maimata karatun.
Ya ce, “Bayan ayyukan cigaban unguwa da muke gudanarwa ta aikin gayya, mukan bayar da agaji ga marasa lafiya, duk da ba wani karfi ke gare mu ba. Muna yin hakan ne kuwa don mara wa gwamnatin jiha baya, dangane da kokarin da take yi da bayar da tallafi ga kungiyoyin da ke fadin jihar”.
Ya ce ya zama wajibi ga kungiyoyi da su dukufa wajen koyar da matasa sana’o’i don dogaro da kansu, lamarin da ya sa ya yaba wa Gwamna Shema kan kafa wajen koyar da matasa sana’o’i.
“Mukan gudanar taron bita don fadakar da matasa kan su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi da zaman kashe wando. Muna shirye-shiryen tura wasu ’ya’yan kungiya zuwa koyon wasu sana’o’in irin na zamani tare kuma da kafa wani asusun da za mu tallafa wa marayu da gajiyayyu. Muna kira ga jama’ar wannan yanki da ma duk sauran masu hannu da shuni da su taimaka don a kai ga cin nasara”. Inji shi.
kungiyar raya Sha’iskawa Katsina na tallafa wa matasa
Shugaban kungiyar raya unguwar Sha’iskawa da kewaye da ke cikin garin Katsina, Mafawakin Majidadi, Alhaji Sani BK ya ce kungiyar ta mike wajen tallafa wa…