Kungiyar Iyaye da Malaman Makaranta (PTA) ta makarantar Model International School ta bai wa makarantar tallafin kayan kimiyya da gadon asibiti da sauran kayayyakin koyarwa da na wasanni da aka kiyasta kudinsu a kan Naira miliyan daya.
Da yake mika kayayyakin ga Shugaban Makarantar, jagoran kungiyar, Malam Sabo Abdullahi Guri, ya ce kungiyar ta kuma sayo katan 70 na taliya da galan-galan na man girki 70 ta raba wa malamai da kananan ma’aikatan makarantar saboda gabatowar Babbar Sallah.
Alhaji Sabo Guri ya ce, sun sayi kayayyakin ne da nufin kara wa daliban karfin gwiwa wajen harkokin koyon karatu da kuma wasanni. Don haka ya shawarci hukumar makarantar ta yi amfani da kayayyakin da kungiyar ta ba su ta hanyar da ta dace.
Da yake karin haske game da irin ayyukan da suka yi a makarantar; ya ce sun gyara dakunan kwanan dalibai da suka samu matsala ta gobara.
Ya ce sun sayi kayan kimiyyar da na wasan kwallon tebur da Badminton da Lawn Tennis, kuma za su gina filin wasan Tennis, inda suke sa ran kashe Naira miliyan biyu.
Ya gode wa gwamnatin jihar, sakamakon gyara dakin kwanan dalibai da gobara ta lalata a kwanan baya; inda ya yi fata sauran kungiyoyin iyayen yara da malamai za su yi koyi da abin da tasu kungiyar tayi wajen tallafa wa makarantunsu.
Da yake mayar da jawabi Shugaban Makarantar Model, Malam Lawan Yusuf Adamu, ya gode wa kungiyar, lura da yanayin kayan da kungiyar ta samar ga makarantar; tare da yin alkawarin raba kayan bisa adalci tare da yin amfani da su yadda suka dace.