Shugaban Kungiyar Ma’aikata reshen jihar Kwara, Mista Abdulyekeen Agunbiade ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta sake duba batun karin albashin ma’aikatan kasar nan.
Shugaban ma’aikatan ya yi kiran ne a garin Ilorin yayin da yake tattaunawa da manema labarai kan halin da kasar take ciki.
Ya kara da cewa kamar yadda dokar ma’aikata ta tanada za a rika duba albashin ma’aikata duk shekara 10.