✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Neman Zaman Lafiya ta gudanar da taro a Kaduna

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna kungiyar Neman Zaman Lafiya ta ce ayyukanta za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da girmama juna…

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna kungiyar Neman Zaman Lafiya ta ce ayyukanta za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da girmama juna a Jihar Kaduna da kasa baki daya. 

kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin da take gudanar da taron kara wa juna sani a kan muhimmancin zaman lafiya da juna da kuma illar rade-radi a Hayin Banki, da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Jihar Kaduna. 

Ayyukan kungiyar wanda ya karade dukan bangarorin Jihar Kaduna, zai taimaka wajen koyar da matasa hanyoyin son juna da zaman lafiya tare da juna ne ba tare da nuna kabilanci ba ko bambancin addini.

Da yake jawabi a wajen taron da kungiyar ta gudanar na Unguwar Hayin Banki, Sarkin Hayin Banki Malam Mahmud Galadima cewa ya yi, “Ilimi shi ne jigon zama lafiya. Duk mai ilimi ko dai na boko ne ko na addini ba zai shiga cikin harkar dabanci ko shaye-shayen miyagun kwayoyi ba. Don haka nauyi ya rataya a kan kuda kuka samu halartar wannan taro wajen taimaka wa sauran ‘yan uwanku matasa da suke cikin wannan mugun hali. 

Shi ma babban ilimin Jumu’a na Hayin Banki Malam Ishak Ibrahim ya tofa albarkacin bakinsa a wajen taron inda ya ce lallai Allah Ya halicce mu daban-daban, amma ba wai bambancin ba ne matsalar, yadda za mu girma juna ne shi ne matsalar, don haka sai ya yi kira da a ci gaba da zaman lafiya da girmama juna. 

Hakazalika, Fasto Alhamdu A. Tukurah a na shi sakon, ya ce dole ne Musulmi da Krista su zauna lafiya da juna, “an halicci mutum ne kafin a halicci addini. Idan muka dubi baya, za mu gane cewa abin da ya hada mu ya fi abin da ya raba mu yawa.” 

Wannan kungiya dai tana gudana ne karkashin tallafin Robert Bosch Stiftung, kuma taken wannan taro na rana daya da ya  gudana a Hayin Banki Kaduna shi ne “Illar rade-radi”.

Daga cikin ayyukan da aka gudanar a wajen taron akwai wasan kwaikwayo inda aka nuna matsala da illar yawo da labarin karya da rade-radi a game da rikici a cikin al’umma.