kungiyar Mata ’Yan Jarida ta kasa (NAWOJ), reshen Jihar Bauchi, ta gudanar da addu’o’i da nasihohi kan zaman lafiya da kuma neman a sako ’yan matan Chibok da ’yan bindiga suka kama a kwanakin baya, tare da fatar Allah Ya dawo da zaman lafiya a Najeriya.
Sakatariyar kungiyar ta kasa, a Shiyyar Arewa maso Gabas, Hajiya Halima Dimis ta bayyana cewa sun shirya taron addu’ar ne a matakin kasa, yadda kowace jiha ke gudanar da nata, inda limaman Kirista da Musulmi da kungiyoyinsu suka halarta.
Ita ma shugabar kungiyar ta Jihar Bauchi, Hajiya Kaltume Shall ta bayyana cewa yin taron ya zama dole don babu abin da ya fi karfin Allah, saboda haka suke neman kowa ya taimaka da addu’a domin samun ingantaccen zaman lafiyar jama’a da walwala su dawo a Najeriya.
Rebaran Lawi Pokti, shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN a Jihar Bauchi ya nemi jama’a a yi hakurin zama da juna domin Allah Ya hada zaman tare a kasar; a guji mugunta da cin zarafin juna da sabon Allah.
Babban Limamin Bauchi, Alhaji Bala Ahmed shi ma cikin jawabinsa ya yaba game da yadda aka shirya taron addu’ar. Ya bukaci musulmi da kirista kowa ya gyara halinsa, ya koma ga Allah domin samun jinkan Allah. Ya roki kowa ya ci gaba da addu’a a wuraren ibadarsa, don Allah Ya gyara mana rayuwarmu ya ciyar da kasarmu gaba.
Shi ma sakataren watsa labaran gwamnatin Bauchi Ishola Micheal ya yaba da shirya taron, inda ya gode wa limaman da suka halarce shi, kuma ya nemi kowa ya ci gaba da addu’ar neman zaman lafiya a Najeriya.
kungiyar NAWOJ ta yi taron addu’ar samun zaman lafiya
kungiyar Mata ’Yan Jarida ta kasa (NAWOJ), reshen Jihar Bauchi, ta gudanar da addu’o’i da nasihohi kan zaman lafiya da kuma neman a sako ’yan…