kungiyar masu manyan motocin dakon kaya ta Najeriya (NARTO) ta nemi gwamnatoci a Najeriya su samar musu wuraren ajiye motoci na dindindin a jihohi da kananan hukumomin manyan birane domin kare yawaitar hadurran manyan motoci a cikin garuruwa.
Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Alkasim Ibrahim Batayya shi ne ya yi kiran a wajen taron kungiyar na kasa da ya gudana a Bauchi, inda ya bayyana matukar aka samar da hanyoyin bayan gari da kuma wuraren ajiye motoci da sauke kayayyaki a cikin manyan birane, hakan zai taimaka wajen raguwar hadurra tsakanin manyan motoci da kanana da kuma mutane da ke amfani da hanyoyi don a kare hasarar rayuka da dukiyoyin jama’a sakamakon hadurran.
Alhaji Alkasim ya nemi gwamnatin tarayya ta sanya kungiyar NARTO cikin hidimominta na cigaban kasa da kuma shirinta na tallafawa da motoci da kuma jari wato Sure-P da ake raba wa wasu kungiyoyi da daidaikun jama’a a Najeriya, domin su samu damar bunkasa arziki da harkokin cigaban ’yan kungiyar.
Ya ce shirin raba motoci da jari na gwamnatin tarayyar abu ne da zai taimaki mutanen Najeriya su bunkasa tattalin arzikinsu, don haka su ma a zamansu na ’yan kasa ya kamata a sanya su cikin masu cin moriyar shirin.
Haka nan ya nemi gwamnatin tarayya ta taimaka wa kungiyar da motocin daukar marasa lafiya domin su rika kai agajin gaggawa a duk inda hatsari ya faru.
Kwamishinan jin dadi da walwalar jama’a na Jihar Bauchi, Alhaji Umar Saleh shi ne ya wakilci Gwamna Malam Isa Yuguda a wajen taron, don haka ya yi alkawarin isar da kokensu ga gwamnatin
Jihar bauchi domin gina hanyoyin bayan gari, musamman wacce za ta tashi daga Miri zuwa Yalwa ta fita Inkil domin manyan motocin da za su wuce Jos ko Gombe ba sai sun ratsa tsakiyar garin Bauchi ba.
Ya kuma yaba wa kungiyar ta NARTO game da yadda suke taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar sufirin kayayyakin amfanin yau da kullum, tare da fatar za su fito da sabbin manufofin sufuri irin na kasashen da suka ci gaba.
kungiyar NARTO ta nemi a gina hanyoyin bayan gari da tashoshi a manyan birane
kungiyar masu manyan motocin dakon kaya ta Najeriya (NARTO) ta nemi gwamnatoci a Najeriya su samar musu wuraren ajiye motoci na dindindin a jihohi da…