✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar NARTO ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya bashi

Sakataren kungiyar Direbobin Tanka (NARTO) ta kasa, reshen Jihar Kebbi, Alhaji Umar Gulumbe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma hukumar daidaita farashin albarkatun…

Sakataren kungiyar Direbobin Tanka (NARTO) ta kasa, reshen Jihar Kebbi, Alhaji Umar Gulumbe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma hukumar daidaita farashin albarkatun man fetur ta kasa (PPPRA) da su hanzarta biyan bashin da masu dakon mai na Arewancin kasar nan ke bi.
Sakataren ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin kungiyar da ke gidan abincin dan-Tila Jega a Birnin Kebbi a makon da ya gabata.
Ya ce kamar yadda suka yi alkawari da hukumar PPPRA, za a rika biyansu Naira dubu dari biyar da goma sha takwas na dako a kan kowace mota guda, sai ga shi daga baya gwamnatin ta maida shi Naira dubu dari uku da tamanin da takwas kuma ba da wata sabuwar yarjejeniya tsakaninsu ba.
Sakataren ya ce,  “Abin haushi ma shi ne bayan yadda suka yi yarjejeniyar za a rika biyan kudin dakon, sai ya kasance ba a biyan kudin da ya kamata, kudin da aka ga dama ake biya, kuma an yi kimanin wata hudu ba a ba mai mota ko sisin kobo ba. Yanzu haka akwai kudade na kusan wata shidda da ba a biya ba. A kan hakan ne duk wasu masu tankokin mai suka ajiye motocinsu, saboda babu riba ga sana’ar.  Ko kudin mai da za ka sha ga motar da hidimar direba da yaransa da gyaranta, kudin da ake biya na dakon ba zai ishe su ba, balantana ma a samu riba. Wannan shi ke kawo tsadar fetur a Arewa. A halin yanzu idan tanka ta tafi Kudu dauko mai, to mai ita yana da gidan mai, idan ya juye, ko Naira biyar ya kara a duk lita, kila kudin dakonsa ya fita”.
A karshe ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kebbi ta tuna alkawarin da ta yi musu na garejin kananan motocin sufuri na zirga-zirga, wanda har yanzu shiru. Ya yi nunin cewa su ma suna ba da gudummuwa wajen ci gaban jihar, musamman ta fuskar samar da kudaden shiga.