kungiyar Muryar Zawarawa da Marayu (bOWAN) ta rarraba tufafin sallah ga marayu sama da dubu daya, a yayin bikin cika shekaru goma da kafuwarta, tare da neman taimakon Naira miliyan 350, don gina gidan marayu da asibiti, wanda aka yi a harabar Gidan Mambayya a birnin Kano.
A jawabinta, shugabar kungiyar, Hajiya Atine Abdullahi ta bayyana cewa sun saba yin taron ne a kowane watan Ramadan don rarraba sababbin tufafi ga marayu da zawarawa domin su yi bikin sallah da shi. Sai ta yaba wa hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), wacce ta bayar da gagarumar gudummawar kayan tufafi da na abinci.
Shugabar ta ce, “kungiyarmu ce ta fara aurar da zawarawa a shekarar 2005, sai ga shi, Alhamdulilllahi, yanzu gwamnati ta dauki wannan tsari ta aurar da mata 1,356 a lokuta daban-daban”. Ta ce suna neman taimakon ne, “Don gina gidan marayu da makarantar sakandaren ’yan mata ta kimiyya da kuma asibiti don amfanin marayu da zawarawa a jihar”.
A nasa jawabin, Sheikh Tijjani Bala Kalarawy, ya bukaci mazaje su rika kai zuciya nesa tare da guje wa saurin sakin mata; su kuma matan ya nemi su kiyaye mutuncinsu na aure wajen yin cikakkiyar biyayya ga mazajensu. Ya nuna muhimmancin kula da maraya a Musulunci.
Shi kuwa jami’in gudanarwa na hukumar NEMA na shiyya, Alhaji Musa Abdallah Ilallah, ya ce sun bayar da gudummawar kayan ne don tallafa wa ayyukan da kungiyar ke gudanarwa.
kungiyar Muryar Zawarawa da Marayu ta raba wa ‘ya’yanta tallafi
kungiyar Muryar Zawarawa da Marayu (bOWAN) ta rarraba tufafin sallah ga marayu sama da dubu daya, a yayin bikin cika shekaru goma da kafuwarta, tare…