kungiyar ’Yan Uwa Mata Musulmi ta kasa (MSO) reshen Jihar Yobe ta raba kayayyakin abinci ga marayu da matan da suka rasa mazajensu don samun saukin gudanar da rayuwa a lokacin azumin bana.
kungiyar ta raba wadannan kayayyakin ne a cibiyar kula da addinin Musulunci da ke garin Damaturu a ranar Litinin.
Shugabar kungiyar Hajiya Gambo Aji Sulaiman wadda mataimakiyarta Malama Jummai Dauda ta wakilta, ta ce wannan yunkuri na tallafa wa marayu da matan da suka rasa mazajensu daya ne cikin ayyukan da gwamnatin Jihar Yobe ke yi na tallafa wa marasa karfi, musamman a lokacin watan Ramadan don wadata su da abin buda baki da sahur.
Ta ce, kashin farko na wannan shirin an samar da kayayyakin abinci ga mutane 60, yayin da nan gaba kuma za su kara samar da ire-iren wadannan tallafin.
Ta tabbatar da cewar nan gaba kadan kungiyarsu za ta sake raba kayayyakin abincin ga marayu da marasa karfi.
Hassana Abubakar wata mata da mijinta ya mutu ya bar mata ’ya’ya hudu ta ce, ta ji dadin wannan shirin rabon kayayyakin, domin kafin wannan lokacin ta rika tunanin halin da ita da ’ya’yanta za su shiga yayin azumin bana.
Ibrahim Hassan wani yaro maraya ya gode wa kungiyar MSO da ta raba musu wadannan kayayyaki.
kungiyar MSO ta taimaka wa marayu da matan da mazajensu suka mutu
kungiyar ’Yan Uwa Mata Musulmi ta kasa (MSO) reshen Jihar Yobe ta raba kayayyakin abinci ga marayu da matan da suka rasa mazajensu don samun…