✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyar matan Kannywood za ta maka Sarkin Waka a kotu

Matan sun ba Sarkin Waka kwana uku ko ya nemi afuwarsu ko su maka shi a kotu.

Kungiyar Matan Kannywood (K-WAN) ta ba mawaki Naziru M. Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, kwana uku da ya fito ya ba su hakuri kan kalamansa na cewar ana lalata da wasu daga cikinsu kafin a sanya su a fim.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, dauke da sa hannun shugabarta, Hajiya Hauwa A. Bello a Kano ranar Talata.

Ta ce kalaman na mawakin ba su dace ba, kuma tana neman ya fito ya ba su hakuri kan kalamansa wanda kungiyar ta kira da batanci da kaskanci.

Ta kara da cewar kungiyar ba za ta nade hannunta ta zura ido mutane na ci gaba da zubar da mutuncin masana’antar ba.

Ta kuma ce sun ba shi wa’adin sa’a 72 ya fito don neman gafararsu, ko kuma su mika lamarin ga kotun shari’ar musulunci don bi musu kadinsu.

Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne Kannywood ta dauki zafi kan batun biyan jaruman masana’antar N2,000 kudin fitowa a cikin fim da Ladin Cima ta yi.

Lamarin da ya janyo cece-kuce sasai, inda a ciki Sarkin Waka ya wallafa wani bidiyo a shafinsana Instagram, inda ya yi zargin cewa baya ga masu fitowa a fim kyauta, akwai matan ma da sai an yi ‘amfani’ da su kafi a saka su.

Sai dai da alama kalaman mawakin bai su yi wa mutane da dama a masana’antar dadi ba.