✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata Musulmi sun nemi Majalisa ta gaggauta kafa dokar sanya hijabi a makarantu

tunda har aka yi dokar sanya takunkumin fuska saboda COVID-19, babu dalilin haramta wa wadanda addininsu ya ba su dama

Gamayyar Kungiyar Mata Musulmi (NMW) ta bukaci Majalisar Dokokin Najeriya ta yi gaggawar kafa dokar sanya hijabi a makarantu.

Jam’iar kiyaye hakkin dan Adam ta Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Miss Amasa Firdause-Aljannah, ce ta bayyana hakan a taron Ranar Hijabi ta Duniya da aka gudanar a Abuja.

“Majalisa ta gabatar da kudirin halasta sanya hijabi a hukumace a ma’aikatu da makarantu na gwamnati da masu zaman kansu.

“Don haka muna kira da babbar murya da gaggauta amicewa da kudirin, domin tunda har za a yi dokar sanya takunkumin fuska saboda cutar COVID-19, babu dalilin haramta wa wadanda addininsu ya ba su dama.

“Tun a watan Maris din 2021 kammala karatu na biyu kan kudurin, don haka yanzu muna tuni,” in ji Firdause.

Ta jaddada muhimmacin majalisar ta yi dokar don kare hakkin masu sanya hijabi a matsayinsu na masu cikakken ’yanci a Najeriya.

Ta kuma roki goyon bayan masu ruwa da tsaki da suka hada da kafafen yada labarai, da gwamnati tun daga Tarayya har zuwa kananan hukumomi, hadi da malamai da masu sarautun gargajiya da kungiyoyi masu zaman kansu.